An yi wa al-Bashir sassauci - Al-Taghyeer

Asalin hoton, AFP
'Yan adawa a Sudan na zargin sassauci a hukuncin daurin shekara biyu da kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.
A ranar Asabar ne wata kotun kasar ta kama tsohon shugaban da laifin mallakar wasu kudaden kasashen waje da suka kai dala miliyan 25 ba bisa ka'ida ba.
Kotun ta ba da umarnin kwace kudaden daga tsohon shugaban da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a watan Afrilu.
Ta kuma ba da umarnin mayar da al-Bashir zuwa inda ake tsare da shi domin ci gaba da bincikarsa kan zargin juyin mulkin da ya kawo gwamnatinsa a 1989.
Sai dai alkalin ya ce kotun ba ta da hurumin daure al-Bashir wanda ya haura shekara 70 a gidan yari, a don haka sai dai a tsare tsohon shugaban a gidan gyara halinka.
Amma jaridar Al-Taghyeer ta masu adawa a Sudan ta ce hukuncin kotu ya yi sassauci ga al-Bashir wanda ya mulki kasar na tsawon shekara 30.
Omar al-Bashir na kuma fuskantar zargin aikata kisan kiyashi da kuma kashe masu zanga-zanga kafin a hambarar da shi a watan Afrilu.

Asalin hoton, Reuters
Lauyoyin al-Bashir da magoya bayansa sun fice daga harabar kotun a lokacin da alkalin ke karanta hukuncin. Magoya bayan nasa sun yi zargin bi ta da kullin siyasa a cikin shari'ar, suna masu kafa hujja da shari'ar Majdi Mahjub Mohamed Ahmed, wanda aka zartar wa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da haramtattun kudaden kasahen waje.
Tuni dai daruruwan magoya bayan tsohon shugaban suka fara zanga-zanga a babban birnin kasar domin nuna adawa da matakin kotun.
Masu zanga-zangar sun ce an sanya siyasa a yadda shari'ar ta gudana inda kuma lauyan Al Bashir din ya ce zasu daukaka kara.











