Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya mika wa majalisa sunan sabon shugaban FIRS
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattijan Najeriya sunan sabon shugaban Hukumar Tara Haraji ta kasar, FIRS domin amincewarta.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu, ya fitar ta ce Buhari ya mika sunan Muhammad M. Nami a matsayin sabon shugaban hukumar.
A watan Agusta ne fadar Shugaban kasa ta aike wa Tunde Fowler wasikar neman bayanai game da dalilan da suka sa yawan kudin haraji ya yi kasa ga gwamnatin Najeriya.
Haka kuma, Shugaba Buhari ya amince da sababbin mambobin hukumar daraktocin FIRS.
Hukumar daraktocin dai ta kunshi mambobi daga yankuna shida na Najeriya da wakilai daga wasu ma'aikatun gwamnati.
Muhammad M. Nami dai kwararre ne a fannin haraji da mulki da akawunta.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Bayero da ke Kano a fannin ilimin zamantakewa a shekarar 1991 sannan ya yi digirinsa na biyu a Jami'ar Ahmadu Bello, inda ya karanci fannin kasuwanci a shekarar 2004.
Ya fara aiki da kamfanin PFK a shekarar 1993. A halin yanzu yana aiki ne da kamfanin Manam Professional Services da ke da rassa a jihohin Kaduna da Abuja da Neja.
Kazalika, mamba ne shi a hukumomin gudanarwar kamfanoni da kwamitoci da dama a Najeriya.
A shekarar 2017, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi mamba na Kwamitin Shugaban Kasa mai binciken kadarorin gwamnati da aka sace a watan Nuwamba.Ana sa rai shugaban FIRS mai ci yanzu, Babatunde Fowler wanda wa'adinsa ya cika a yau Litinin 9 ga watan Disambar 2019, zai mika shugabancin hukumar ga babban darakta a hukumar daraktoci.
Wanda aka bai wa zai ja ragamar ayyukan hukumar kafin majalisa ta amince da sabon shugaban.