Timi Frank: Osinbajo ya maka mutum biyu a kotu

An wallafa

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya maka wasu mutum biyu kotu bisa zargin bata masa suna da ya ce sun yi.

A shafinsa Facebook, Farfesa Osinbajo ya wallafa cewa "a 'yan kwanakin nan da suka gabata, wasu tsirarun mutane sun ta yada karerayi a kaina a kafafen watsa labarai."

Ya kara da cewa "a yau na shigar da mutanen biyu kara kotu wadanda su ne suke yada wadannan karerayi."

'Zan kawar da duk wata rigar kariya da tsarin mulki ya ba ni domin ganin an bi min hakkina dangane da bata min suna da yi min karya da aka yi."

Wannan dai ba ya rasa nasaba da zargin da tsohon mataimakin sakataren watsa labaran jam'iyyar APC Timi Frank ya yi yayin wata hira da wata kafar watsa labarai.

Jami'in ya yi zargin cewa hukumar tattara haraji ta kasar, FIRS, ta bai wa mataimakin shugaban kasar biliyoyin naira domin yin kamfe a zaben 2019.

Mutanen kuma sun yi zargin cewa batun kudin da FIRS ta bai wa mataimakin shugaban ne ya jawo rashin jituwa tsakanin Osinbajo da wasu mukarraban gwamnati a fadar shugaban kasa.