Zanga-zangar kin jinin gwamnati ta sa an kashe mutum 13 a Iraki

Asalin hoton, Getty Images
Mutane 13 ne suka mutu a zanga-zanga ta baya-bayan nan a kudancin birnin Nasiriya na kasar Iraki.
A ranar Alhamis jami'an tsaro sun budewa masu zanga-zanga wuta da harba hayaki mai sa hawaye a kokarin tarwatsa masu boren, inda mutane 70 suka jikkata.
'Yan Iraki na yi wa gwamnati tawaye, inda suke bukatar gwamnati ta samar da ayyukan yi, da kawo karshen cin hanci da rashawa da kara inganta walwalar jama'a.
A ranar Laraba gungun masu zanga-zangar sun fito kungiya-kungiya tare da bankawa wajen ofishin jakadancin Iran da ke birnin birnin wuta, wanda a birnin ne hukumomin mabiya mazahabar shi'a kuma jami'an gwamnati suke, sannan a can ne aka binne Imam Ali, daya daga cikin sahabbai kuma suruki ga Manzon Allah SAW.
Sojojin Iraki sun sanar da kafa kurkukun soji don magance tsagerancin masu zanga-zanga.
Rundunar sojin ta ce tuni aka kafa sashen gaggawa da nufin tabbatar da doka da oda da samar da tsaro.
''Kamar yadda kwamandan askarawan Iraki kuma Firai Minista Adel Abdel Mahdi ya sanar, an nada wasu kwamandoji da za su kula da kurkukun don shawo kan tabarbarewar tsaro da masu zanga-zanga ke haddasawa, kwamandojin za su taimaka wa gwamnati don cimma manufar wanzar da zaman lafiya,'' in ji sanarwar.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa tuni aka shawo kan masu zanga-zanga a birnin Nasiriya, amma wasu na far wa 'yan sanda a titunan wasu biranen.
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati dai na son ganin an sauke shugabannin siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa da rashin tabuka abin a zo a gani a kasar.
Yawanci dai sun fusata kan yadda kasar Iran ke katsalandan a harkokin cikin gida na Iraki, inda suke zargin ya karawa kasar koma baya musamman kan takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakaba wa kasar, tun shekarar 2003 da aka hambarar da gwamnatin marigayi Saddam Hussein.
A ranar Laraba an kai wa jakadan Iran a kasar hari a birnin Najaf. Masu boren na zargin Iran din tana kara dagula lamura, ta yadda Irakin ke kwaikwayon salon mulkinsu da gagara magance rashawa.
Shin me ya faru a birnin Najaf?
A ranar Laraba gungun masu zanga-zangar sun fito kungiya-kungiya tare da bankawa wajen ofishin jakadancin Iran da ke birnin birnin, wanda nan ne hukumomin mabiya mazahabar shi'a kuma jami'an gwamnati suke, sannan a nan ne aka binne Imam Ali, daya daga cikin sahabbai kuma suruki ga Manzon Allah SAW.
Masu zanga-zangar na rera waken da ke cewa ''Dole Iran ta fice daga Iraki,'' yayin da wuta ke tartsatsi a wajen ofishin diflomasiyyar.

Asalin hoton, AFP
Wutar ta yadu har harabar ofishin, wani ma'aikaci ya tsira da ranshi bayan masu boren sun shiga ciki. Gwamnatin Iraki ta yi Allah-wadai da harin tare da cewa hakki ya rataya a wuyanta na kare ofishin da jami'an diflomasiyya.
Wannan shi ne karo na biyu cikin wata guda da aka kai hari ofishin jakadancin Iran a kasar, bayan wanda aka kai birnin Karbala cibiyar mabiya mazahabar shi'a makwanni uku da suka gabata.
Me ya fara haddasa rikicin?
Sama da shekara daya kenan da Shugaba Abdul Mahdi ya hau karagar mulki, inda ya yi alkawarin sauye-sauye don inganta walwalar 'yan kasa.
Matasan Iraki da suka gaji da gafara sa ba su ga kaho ba, musamman da shugaban ya kasa magance rashin aikin yi da ya yi wa matasan Iraki dabaibayi, da rashin kulawa a asibiti, babu hanyoyi da tsadar kayan masarufi, da cin hanci da rashawa tsakanin jami'an gwamnati.
Wadannan dalilai da ma wasu sun tunzura matasan suka fito titunan kasar don yin zanga-zanga musamman a biranen Basra, da Bagadaza da Nasiriyya daga bisani kuma suka mamaye sauran garuruwa da biranen kasar.
Bayan shafe kwanaki shida suna zanga-zanga, an kashe a kalla farar hula 149, kuma Mista Mahdi ya yi alkawarin yi wa majalisa garanbawul, da rage albashin manyan jami'an gwamnati da sanar da fito da wani shiri da zai samawa matasa ayyukan yi.
Sai dai masu boren sun ce babu abu guda daya da shugaban ya yi cikin alkawuran da ya yi musu, don haka suka sake bazama tituna don ci gaba da zanga-zangar a karshen watan Oktoba.
Zanga-zangar ta karade kusan baki dayan kasar Iraki, sun kara fusata lokacin da jami'an tsaro suka yi amfani da karfin tuwo don tarwatsa su, daga bisani suka fara yi musu harbin kan mai tsautsayi.
Shugaban Iraki Barham Saleh ya ce lallai sai Abdul Mahdi ya yi murabus matukar jam'iyyun siyasa suka amince maye gurbinsa da wani.












