Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda taron tona wa matsafa asiri ya janyo ce-ce-ku-ce a Enugu
Mabiya kungiyar addinin kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria sun yi zanga-zanga don tilasta wa jami'ar Najeriya ta Nsukka sauya sunan taron kolin da ta shirya kan matsafa da maita.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Bishop Godwin Madu, ta ce ba za su nade hannu suna gani a mika jihar ga matsafa da mayu ba.
Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) ta ayyana kwanaki biyu domin yin addu'o'in neman wadanda suka shirya taron su soke shi.
To sai dai masu jawabi a wurin taron sun ce idan babu tsafi to da coci-coci ba su samu abin yi ba kasancewar hanyar da fasto-fasto ke bi kenan wajen juya akalar mutane.
Wadanda suka shirya taron ba su soke taron ba amma sun sauya masa suna zuwa 'Sauye-Sauyen Halayyar Dan Adam'.
Taron dai wanda wata cibiyar nazari a jami'ar ta shirya shi ne irinsa na farko a Najeriya.
Tsafi da maita dai na daya daga cikin camfe-camfen mutanen Afirka, inda suke danganta cututtuka da maita ko tsafi.