Hadarin jirgin sama ya kashe mutane da dama a Congo

Asalin hoton, @eliezaireushin
Mahukunta sun ce akalla mutum 24 ne suka mutu bayan da wani jirgin sama ya fada kan gidajen al'umma a garin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Daga cikin wadanda suka mutu har da mutum hudu wadanda jirgin ya fada kan gidansu.
Gwamnan yankin arewacin Kivu, Nzanzu Kasivita ya ce karamin jirgin ya tokari kasa ne a unguwar Mapendo, bayan ya gaza tashi yadda ya kamata da safiyar Lahadi.
Hukumomi sun ce jirgin na dauke ne da fasinjoji 17 da kuma ma'aikata 2.
Ana yawan samun hadurran jirgin sama a kasar ta DR Congo saboda karancin bin ka'idojin kariya da rashin kula da lafiyar jirage, tuni ma aka haramta wa dukkanin jiragen saman kasar yin balaguro zuwa kasashen tarayyar Turai.
Mene ne sanadin hadarin?
Wata majiya a filin jirgin sama na garin Goma ta shaida wa BBC cewa jirgin mai lakabin 'Dornier-228 twin-turboprop' mallakin wani kamfanin sufurin jiragen sama na kasar da ake kira Busy Bee - ya fado kasa ne mintuna kadan bayan tashin sa.
Jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa garin Beni, mai nisan kilomita 350 daga Goma.

Asalin hoton, Reuters
Wakilin BBC ya ce ba a riga an tantance abin da ya haifar da hadarin ba, sai dai wata majiyar na cewa jirgin ya samu matsalar inji ne jim kadan bayan tashin sa.
Masu aikin ceto da sauran al'umma sun garzaya wurin da abin ya faru domin taimaka ma wadanda suka raunata da kuma zakulo gawarwaki.
Babu tabbas kan yawan mutanen da ke cikin gidajen da jirgin ya fada a kansu.











