Amurka ta amince Isra’ila ta ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa

Gabar Yamma da Kogin Jordan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Isra'ila ta gina sabbin matsuguni sama da 100 a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Birnin kudus
An wallafa

Amurka ta sauya matsayi kan matsugunan Yahudawa da Isra'ila ke ginawa a yankunan Falasdinawa, wadanda ta ce ba su saba dokar kasashen duniya ba.

Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce makomar gabar Yamma da Kogin Jordan ya kasance wani mataki ga Isra'ila da Falasdinawa su sasanta.

Isra'ila ta yi maraba da wannan mataki na Amurka - wanda saba matsayin Amurka zamanin Barack Obama wanda shugaba Trump ya gada.

Amma Saeb Erekat babban mai shiga tsakani daga bangaren Falasdinawa ya ce matakin Amurka babbar barazana ce ga tsaro a duniya, da kuma abin da ya kira "karan tsaye ga dokokin duniya"

Isra'ila na gina sabbin matsugunan ne a yankunan da ta mamaye a yankin gabas ta tsakiya a 1967

Wannan matakin amincewa da matsugunan na Amurka ya rusa manufar ma'aikatar wajen kasar ta tsawon shekara 40.

A shekarar 1978 ne ma'aikatar wajen Amurka ta fitar da wani ra'ayin doka da ke bayyana cewa matsugunnan sun sabawa dokokin kasashen duniya.

A cikin sanarwar da ya bayar, Sakataren wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce "Amurka ta yanke shawarar cewa matsugunnan da Isra'ila ta gina a Yamma da Gabar kogin Jordan ba su saba dokar kasa da kasa ba."

A shekarar 1978, gwamnati Carter ta zartar da matsayin cewa kafa matsugunan fararen hula da Isra'ila ta yi ya saba da dokokin kasashen duniya.

Sai dai a shekarar 1981 Shugaba Reagan ya bayyana rashin yarda da matsayin. Inda ya nanata cewa shi bai yarda da cewa kafa matsugunan, haramtaccen abu ba ne.

Sai kuma gwamnatocin da suka biyo baya sun amince cewa ci gaba da aikace-aikacen kafa matsugunan na iya zama wani tarnaki ga zaman lafiya,

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "matakin ya yi daidai" tare da yin kira ga sauran kasashe su yi koyi da Amurka.

Mene ne rikicin mamayar Isra'ila

Construction work at Israeli settlement of Efrat (Feb 2016)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Israel's prime minister has vowed never to remove settlements

Gine gine a Gabar Yamma da Kogin Jordan sun dade suna zama tushen rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Kimanin Yahudawa 600,000 ke zaune a matsugunin da Isra'ila ta gina a Yamma da Kogin Jordan da kuma birnin Kudus.

Gine-ginen dai ana ganin sun saba dokar kasashen duniya, zargin da Isra'ila ta dade tana musantawa.

An dade Falasdinawa na kiran a dakatar da gine-ginen, wani abu da suke ikirarin zai hana su samun 'yancin cin gashin kai.

Presentational grey line