Ana sasantawar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Gaza

Asalin hoton, Reuters
An fara sasantawar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da mayakan sa kai na Falasdinu da ke Gaza, bayan shafe kwana biyu ana mummunan fadan da ba a yi irinsa ba cikin watannin da suka gabata.
Majiyoyin Masar da na Isra'ila sun ce an fara yarjejeniyar tsagaita wutar ne da misalin karfe 3.30 na tsakar dare agogon GMT. Isra'ila ta ce ta cimma manufofinta.
Kafin a gama fadan, an kashe wasu mutum takwas na iyali daya a wani harin saman Isra'ila a Gaza, kamar yadda Falasdinawa suka ce.
Majiyoyin yankin sun ce Falasdinawa 32 ne suka mutu a fadan, wanda aka fara sakamakon kashe wani jagoran mayakan sa kai.
Isra'ila ta ce fiye da mutum 20 na wadanda suka mutu din mayakan sa kan Falasdinu ne.
Sannan wasu gomman Falasdinawa da Isra'ilawa sun ji raunuka, a cewar majiyoyin lafiyar bangarorin biyu.
Kungiyar mayaka masu fafutukar jihadi ta Falasdinawa PIJ, ta harba roka fiye da 400 Isra'ila, a cewar Isra'ilan, yayin da ita kuma ta kai hare-haren sama kan abin da ta kira ramuwar gayya ce kan kungiyar PIJ.
Rikicin ya fara ne bayan da Isra'ila ta kashe wani babban kwamandan kungiyar PIJ Baha Abu al-Ata a wani hari da aka kai gabanin asuba ranar Talata.
Isra'ila ta ce shi ne ke da alhakin wasu rokoki da aka harba mata daga Gaza kuma ya shirya sake kai wasu.
Mummunan fadan da aka yi cikin kwana biyu ya fi kamari ne a ranar Laraba da daddare, a lokacin da wani harin saman Isra'ila ya fada kan wani gida a Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza, inda mutum takwas 'yan gida daya suka mutu.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza, wacce kungiyar mayakan sa kai ta Hamas ke kula da ita, ta ce dukkan wadanda suka mutun fararen hula ne, da suka hada da wata mace da wani yaro.
Sojojin Isra'ila sun ce harin saman ya kashe kwamnadan PIJ Rasmi Abu Malhous, wanda ta ce shi ne babban mai kula da bangaren rokoki.
Bayan fara sasantawar, wakilin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na Gabas Ta Tsakiya Nickolay Mladenov, ya ce da MDD da Masar sun yi aiki tare don kare irin munin da rikicin zai iya yi a ciki da wajen Gaza wanda zai iya zama yaki."
A wani sakon Twitter, ya yi kira ga dukkan bangarorin biyu da su "nuna jajircewa su kuma kare zubar da jini."











