Najeriya ta fi yawan yaran da cutar pneumonia ke kashewa —UNICEF

Asalin hoton, AFP
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce a tsakanin kasashen duniya, Najeriya ce ta fi yawan yaran da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar pneumonia.
Rahoton, wanda Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar, UNICEF, ta wallafa, ya ce a bara an kiyasta cewa yara 162,000 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar (wato yara 443 a kullum, ko kuma yara 18 a duk sa'a guda).
"Pneumonia cuta ce mai kisa", inji Pernille Ironside, wakiliyar Hukumar ta UNICEF a Najeriya, "kuma tana daukar rayukan yara da dama duk da cewa galibi za a iya hana faruwar hakan".
Rahoton ya kuma ce daga cikin adadin yaran da suka mutu a 2018 a Najeriya, kashi 19 sun mutu ne sakamakon pneumonia.
"Amma duk da haka, kusan an yi shakulatin bangaro da wannan cuta mai kisa a tsare-tsaren kiwon lafiya na kasashe da ma na duniya baki daya", inji Ms Ironside.
Cutar da kan shafi huhu
Hukumar ta UNICEF ta ce karancin abinci mai gina jiki da shakar hayakin itace da ake konawa wajen dafa abinci na taimakawa wajen ta'azzara kamuwar cutar.
Baya ga Najeriya, kasashen da ke kan gaba wajen mutuwar yara sakamkon cutar sun hada da Indiya da Pakistan da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da kuma Habasha.
A watan Janairu ne kungiyoyi da hukumomi za su gudanar da taron duniya a Spain domin tattaunawa a kan yadda za a shawo kan cutar.
Kasashen da cutar pneumonia ta fi kisa
Hukumar UNICEF ta bayyana jerin kasashen da cutar pneumonia ta fi kisan yara 'yan kasa da shekara biyar a 2018:
1. Najeriya 162,000
2. Indiya 127,000
3. Pakistan 58,000
4. Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo 40,000
5. Habasha 32,000
6. Indonesiya 19,000
7. China 18,000
8. Cadi 18,000
9. Angola 16,000
10. Tanzaniya 15,000
11. Somaliya 15,000
12. Nijar 13,000
13. Mali 13,000
14. Bangladesh 12,000
15. Sudan 11,000
Jimilla a duniya 802,000












