Iran za ta sake 'karya' yarjejeniyar 2015 ta nukiliya

Handout photo from the Atomic Energy Organisation of Iran showing advanced centrifuges at the Natanz uranium enrichment facility in Iran (4 November 2019)

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Iran za ta fara saka iskar gas cikin na'urar da ake amfani da ita wajen inganta sinadarin uranium dinta a ranar Laraba, wanda hakan ya kara saba wata yarjejeniya cikin yarjejeniyoyin da aka yi da ita a 2015 kan nukiliya.

Shugaba Hassan Rouhani ya bayyana cewa za a iya fasa daukar wannan matakin idan kasashen duniya suka yi abin da ya ce.

Sindarin Uranium din da aka inganta za a iya amfani da shi domin yin makamashin nukiliya da kuma makaman nukiliya.

Wannan shi ne mataki na hudu da Iran din ta dauka tun a watan Yuli wanda wannan na cikin matakan da ta dauka na mayar da martani ga Shugaban Amurka Donald Trump kan takunkumin da ya kakaba mata.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a 2015, Iran ta amince da takaita ayyukanta na nukiliya da kuma bada dama ga masu sanya idanu kan nukiliya na duniya domin duba ayyukanta wanda hakan zai sa a cire takunkuman da aka kakaba mata.

Sai dai Mista Trump ya fita daga yarjejeniyar a bara inda ya nemi ya tilasta wa Iran ta saka hannu a wata yarjejeniya da za ta bada damar sa ido da bin diddigi kan duk wani motsi da Iran din ta yi dangane da nukiliyar da kuma dakatar da ita kan kera makamai masu linzami.

Iranian President Hassan Rouhani speaks at the Noavari factory in Tehran, Iran (5 November 2019)

Asalin hoton, EPA

Sai dai Iran din duk ta ki amincewa da wadannnan bukatun na Amurka.

Kasashen da suke cikin yarjejeniyar da suka hada da - Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha - sun yi kokarin ganin yarjejeniyar ta dore, sai dai wannan takunkumin ya janyo kasuwar mai ta Iran ta durkushe, darajar kudin kasar ta kare da kuma hauhawan farashi.

Iran dai ta dage kan cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.

Kafin 2015, kasar na da wuraren inganta sinadaren guda biyu - Natanz da kuma Fordo.