An tsige mataimakin gwamnan Kogi

mataimakin gwamnan Kogi da aka tsige Simon Achuba

Asalin hoton, @Simon Achuba

An wallafa

Majalisar dokokin jihar Kogi da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ta tsige mataimakin gwamnan jihar daga mukaminsa.

An tsige Simon Achuba daga mukaminsa na mataimakin gwamnan Kogi bayan zarginsa da rashin tafiyar da aikinsa yadda ya kamata tare da tozarta gwamnan jihar Yahaya Bello da kuma jam`iyyarsu ta APC.

Majalisar dokokin jihar Kogin ta yanke shawarar tsige Mista Achuba ne bayan ta karbi wani rahoto daga wani kwamitin da babban jojin jihar ya kafa, wanda ya gudanar da bincike a kan zargin da ake yi masa.

Sai dai Simon Achuba ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa.

Kudurin tsige mataimakin gwamnan dai ya samu amincewar mafi yawan 'yan majalisar, kamar yadda daya daga cikin 'yan majalisar dokokin Hon Isa Umar ya shaida wa BBC.

Ya ce sun tsige shi ne saboda rashin gamsuwa da yadda yake gudanar da aiki yadda ya dace.

An shafe lokaci ana takun-saka tsakanin tsohon mataimakin gwamnan da gwamna Yahaya Bello da jam`iyyar APC, lamarin da har ta kai aka dakatar da shi daga jam'iyyar APC.

Wasu rahotanni sun ce sun samu sabani da gwamnan a kan yadda ake shugabantar jihar.

Wannan dabambarwar na zuwa yayin da ya rage saura wata guda a yi zaben gwamna a jihar ta Kogi.