Masu fama da tarin fuka sun ragu - WHO

Hoton kirjin mai fama da tarin fuka

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ta yi nasarar yaki da cutar tarin fuka kuma mutum miliyan bakwai aka iya warkarwa daga cutar - adadin da ya haura na shekarar 2017.

WHO ta ce adadin wadanda aka warkar ya haura na shekarar 2017 inda aka yi nasarar jinyar mutum miliyan shida da dubu dari hudu.

Rahoton na WHO, ya nuna cewa an samu raguwar mutanen da suke mutuwa sanadiyyar kamuwa da cutar kasancewar mutum miliyan daya da dubu dari biyar ne suka mutu a shekarar da ta wuce, sabanin mutum miliyon daya da dubu dari shida da suka mutu bara.

Hukumar lafiya ta duniyar ta alakanta nasarar da aka samu da yadda ake gano mutanen da suke harbuwa da cutar da kuma ingancin maganin da ake musu.

Sai dai hukumar ta kara da cewa ba a yi katarin gano dukkan mutanen da ke harbuwa da cutar tarin fukar da aka yi harin cimma wa ba a duniya, kasancewar har yanzu akwai kimanin mutum miliyan uku da ke fama da cutar.

Rahoton na WHO ya bayyana kasashe takwas a duniya da suka fi yawan mutanen da ke fama da cutar tarin fuka a duniya a shekarar da ta wuce, wadanda suka hada da Bangladesh da China da Indiya da Indonesiya da Najeriya da Pakistan da Philippines da kuma Afirka ta kudu.

WHO ta ce rashin tsarin kiwon lafiya mai nagarta na daga cikin matsalolin da ake fuskanta a kasashe da dama wajen gano masu kamuwa da cutar da jinyar da ake musu.

Ta ce wannan ya sa mafi yawan masu harbuwa da cutar a irin wadannan kasashe na shiga wani hali, kasancewar kashi 20 cikin dari na abin da suke samu na karewa ne wajen jinya.

Rahoton ya jaddada muhimmancin inganta bincike da samar da karin kudi don ci gaba da yakin da ake yi da cutar, musamman ma a shekarar 2019, saboda rahoton ya nuna cewa akwai gibi ta fuskar kudi.

Hukumar lafiyar ta kiyasta cewa ana bukatar cike gibin da ya kai dala biliyon uku da miliyon dari uku na kudin da ake bukata don yin kariya ga cutar tarin fuka a duniya.

Sai dai duk da wannan kalubalen, wannan nasarar da aka samu a bara ta kara wa hukumar ta lafiya kwarin-gwiwar cewa za a iya cimma muradin da ake da shi na dakile cutar tarin fuka a duniya nan da shekara ta 2030, musamman ma idan aka samu hadin-gwiwar da ake bukata daga dukkan bangarorin da lamarin ya shafa.