Saudiyya: Masu Umrah 35 sun mutu a hatsarin mota

Asalin hoton, AFP
Mutum 35 'yan kasashen waje sun rasa rayukansu wasu hudu kuma suka ji raunuka sanadiyyar hatsari da wata motar bas ta yi a kusa da birnin Madina dake Yammacin kasar Saudiyya.
Bas din ta yi taho-mu-gama ne da wata motar daukar kaya a al-Akhal da misalin karfe 7:00 na yamma agogon kasar a ranar Laraba, karfe 5:00 kenan agogon Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa abin ya rutsa ne da Larabawa baki da wasu 'yan kasashen yankin Asiya a kan hanyarsu ta zuwa aikin ibada daga Makka zuwa Madina.
Zuwa yanzu ba a iya tabbatar da kasashen da suka fito ba, sai dai Fira ministan Indiya ya ce "ya kadu" da jin labarin hatsarin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yarima Faisal bin Salman Al Saud, gwamnan Madina, shi ma ya yi ta'aziyya ga iyalan mamatan.
Mutum hudu da suka tsira da raunuka an kai su asibitin al-Hamna a birnin Madina. Mahukuntan Saudiyya sun kaddamar da bincike game da lamarin.
Wasu hotuna da wata kafar yada labarai a kasar ta wallafa sun nuna wata motar safa mai hawa biyu tana ci da wuta a kan titi tagoginta a farfashe.
Jaridar The Okaz ta ruwaito cewa fasinjojin motar sun fita ne domin gudananar da aikin Umrah.

A shekarar da ta gabata wasu mutum hudu 'yan kasar Birtaniya dake aikin Umrah sun mutu, wasu 12 suka ji rauni bayan da wata babbar motar dakon mai ta doke motar safa da suke tafiya a ciki.
Haka kuma wasu 'yan Birtaniyar shida sun mutu a shekarar 2017 a kan hanyarsu ta zuwa Madina daga Makka bayan da tayar motarsu ta fashe.











