Uber ya fara jigilar fasinja da jirgin ruwa a Legas

Uber boat

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Kamfanin sufurin nan da ake kira UBER da ke amfanin da hanyoyin sadarwa domin daukar hayar motocin ga masu bukata, a yanzu ya fara zirga-zirgar fasinjojin ta hanyoyin ruwa a birnin Legas.

Jihar Legas dai na da yawan bil'adama wadanda kuma da yawa kan yi amfani da hanyoyin ruwa inda wa su lokutan su kan zo da kifewar jirgi tare da salwantar rayuka.

Kamfanin na Uber dai na karbar kudi da bai haura naira dari biyar ba, akan kowanne hawa ko sauka.

Ko da yake tsarin jigilar fasinjoji ta ruwa dai dadadden abu ne a yankunan da ke gabar teku a Legas, to sai dai hakan na ciwa fasinjoji da hukumomi tuwo a kwarya, sakamakon yadda ake yawaita samun hatsari da kan zo da salwatar fasinjoji.

Wannan ne ya sa gwamnatin jihar Legas ta tashi haikan domin ganin in mai yiwuwa ce su hada hannu da kamfanonin sufuri na ciki da wajen kasar domin lalubo hanyoyin da za a habaka harkokin sufurin ruwa - kamar yadda kamfanin UBER din na kasar waje ya fara jigilar fasinjoji a wasu yankunan a Ikko.

A yanzu ana samun jiragen ruwan fasinja na Uber daga Ikorodu zuwa birnin Legas da Ikoyi da kuma Apapa kafin a kara fadada ayyukansa.

Kamfanin Uber ya kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji ta mota domin daukar haya shekaru uku da suka gabata.

Fasinjoji da aka yi samar da tsarin jirgin ruwa dominsu sun nuna jin dadinsu matuka.

Tun ba yau ba ne ake ta samun rahotannin matsalolin kifewar jiragen ruwa dauke da mutum ko dai 20 ko 30 da kalilan ne kan samu tsira.

Mutane sun gwammace amfani da hanyoyin sufuri ta ruwa saboda saukin kudi da kuma yanke matsalolin cuncokosn ababan hawa da kan haifar da tafiya ta kasa gaba ta kasa baya.

An sha samun aukuwar hatsarin jiragen ruwa a wasu sassan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An sha samun aukuwar hatsarin jiragen ruwa a wasu sassan Najeriya

Hakan na zama babbar matsala ga ma'aikata da ke shirin zuwa aiki ko kuma bayan kulle aiki a rana.

Su ma jami'an da ke kula da harkokin jirgin sun tabbatar da cewa sun mayar da hankali a kan abubuwa da ke kai wa suna dawowa da fasinjoji da kuma lafaiyar jirgin.

Kamfanin ya kuma ceaya tanadin kayayyakin kare fasinjojin daga nutsewa a cikin ruwa idan jirgi ya samu matsala.

Gwamnatin jihar Legas ba ta boye jin dadinta ba, bisa la'akari cewa ta dade tana ta fafutukar inganta harkokin sufuri kama daga na mota har zuwa na ruwa - wani abu da aka fara shaida nasararsa da aka kaddamar da motocin haya a karkashin gwamnatin jihar.

Ko da yake nasarar har yanzu ba ta wadatar da miliyoyin al'ummar jihar ba, amma dai akwai ci gaba da babu tsararta a Najeriya.

Wasu al'ummar jihar na cewa tsari ne mai kyau amma suna fatan farashin zirga-zirgar jiragen haya na Uber ba za su yi tsada har can ba.

A shekarar 2017 ne kamfanin Uber ya kaddamar da jigilar fasinjoji ta ruwa a kasar Masar.