Kotun sauraron kararrakin zabe za ta raba gardama kan zaben gwamna na Kano da Sokoto

An wallafa

A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a jihohin Kano da Sokoto za ta yanke hukunci kan shari'ar da ake tsakanin gwamnonin jihohin masu ci da abokanan hamayyarsu.

A shari'ar da ta shafi zaben Kano na ranar 9 ga watan Maris, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da 'Abba-Gida-Gida' ne ke fafatawa a gaban kotun karkashin mai shari'a Halima Shamaki.

Dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ya shigar da karar, inda yake kalubalantar nasarar da Abdullahi Umar Ganduje ya samu a matsayin wanda ya ci zaben gwamna da aka yi bana.

Ganduje ya ci zaben ne na biyu da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.

Idan aka hada sakamakon zaben na farko da na biyu, jimilla APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya ci zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Kano na ranar Asabar 9 ga watan Maris, a matsayin wanda bai kammala ba, lamarin da ya kai ga zagaye na biyu.

A jihar Sokoto ma, kotun sauraron koke-koken zaben na dab da yanke hukunci kan shari'ar da dan takarar jam'iyyar APC Ahmed Aliyu ya shigar, inda ya kalubalanci zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Tambuwal ya yi nasara a zaben Sokoton da kuri'u 512,002, bayan da ya doke abokin hamayyarsa, Ahmed Aliyu da ya samu kuri'u 511,660.

Duk wanda hukuncin da ake sa ran bayyanawa a yau bai yi wa dadi ba to yana da damar daukaka kara.