China na bikin cika shekara 70 na kafuwar mulkin Kwaminisanci

An wallafa

China na wani kasaitaccen biki domin zagayowar ranar da aka kafa jamhuriyar jama'ar China shekaru 70 da suka gabata.

Ranar 1 ga watan Oktoba 1949 ne Mao Zedong - wanda aka fi sani da Chairman Mao - ya sanar da kafuwar sabuwar jamhuriyar ta China.

Wannan ya biyo bayan nasarar da sojoji masu ra'ayin kwaminisanci suka yi a yakin basasar kasar da aka yi.

Wannan sabuwar jamhuriyar ta sami gagarumin bunkasa, amma kuma kasar ta kasance mai matukar takura wa al'umominta.

A halin da ake ciki, ana can ana wani kasaitaccen faretin sojojin kasar, kuma a na sa ran Shugaba Xi Jinping zai yi jawabi.

Dakarun soji 15,000 na can a dandalin Tiananmen da ke tsakiyar birnin Beijing, kuma ana tallata sababbin kayayyakin yakin da kasar ta kera.

Mene ne makasudin wannan bikin?

Shekaru saba'in da suka gabata, Chairman Mao ya sanar da kafuwar sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin bayan da jam'iyyar Kwaminisanci ta sami galaba kan jam'iyya mai mulkin kasar a wancan zamanin mai suna Kuomintang.

Tun shekarun 1920 bangarorin biyu ke gwabza yakin basasa.

Wannan muhimmin mataki ne ya samar wa China alkiblar da ta ke kai a yanzu, kuma ta sami karuwar arziki da ikon fada a ji a duniya.

China ta ce tana samar da wani sabon tsarin siyasa ne - wato tsarin gurguzu amma irin na China - kuma tsarin ya fitar da miliyoyi daga kangin talauci.

An shirya kasaitaccen fareti

China za ta baje kolin makaman yaki masu yawa, ciki har da motoci masu sulke na yaki da makamai masu linzami.

Fiye da jiragen yaki 150, cikinsu akwai masu fasahar boye wa daga abokan gaba, za su rika watayawa a sararin samaniyar birnin Beijing.

Daga baya kuma ana sa ran fararen hula 100,000 za su gudanar da wasanni masu kayatarwa. Cikinsu akwai manoma, da likitoci da daliban makaranta.

Bayan rana ta fadi kuma za a yi wani bikin wake-wake a dandalin Tiananmen.