Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Dillalan motoci a Najeriya na cikin tasku a hannun kwastan'
Masu dillancin motoci a sassan jihar Legas dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da jami'an hukumar kwastam suka rufe musu kasuwancinsu bisa zargin sun shigar da motoci ta barauniyar hanya sun yi tur da abin da suka kira cin zarafi da yunkurin jami'an hukumar kwastam na ayyana su a matsayin 'yan smoga.
Dillalan motocin sun kuma yi Alllah wadai da yadda ake rufe musu kasuwancinsu abinda ke haifar musu da asara mai yawa tun bayan da gwamnati ta kudiri aniyar yaki da masu shigo da motocin ta barauniyar hanya.
A cewar dillalan, 'su 'yan kasa ne na gari da ke bada tasu gudunmawar wajen habaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar baiwa dunbin al'umma ayyukan yi baya ga kudin fito da ya kai naira biliyan 20 da ya ke tafiya asusun gwamnatin tarayya.
Sai dai daya daga cikin manyan masu motocin a kamfanin Stallion, Arpita Luthra, ya musanta zargin da ake cewa sumamen na jami'an hana fasa kwaurin ya shafe shi.
Shi ma shugaban sashen kasuwanci na kamfanin, Arpita Luthra, a cewar jaridar 'The Punch' ya ba wa hukumar hana fasa kwaurin ya yi bisa namijin kokarin da ya ce tana yi na ganin ta tsaftace harkar dillancin motoci a Najeriya.
Abiona Babarinde shi ma mai sana'ar shigar da motoci zuwa Najeriya ne, ya ce kamfaninsu na Coscharis na tafka asara mai dunbin yawa sakamakon rufe kasuwancin nasu da hukumomi ke yi.
Ya ce sumamen da hukumar kwastan take kaiwa kan kasuwancinsu ya yi hannun riga da kudirin gwamnatin tarayya na ganin ta jawo hankalin masu zuba jari da saukaka wa 'yan kasuwa gudanar da kasuwancinsu cikin sauki.
Shi kuwa wani dillali a Ikeja da ke jihar Legas ya ankarar da hukumar ta kwastam cewa 'Najeriya ba a karkashin mulkin soji ta ke ba da za a rika rufe kasuwancin mutane ba tare da basu takardar gargadi ba.
Hukumar hana fasa-kwaurin dai ta ce tana kai wadannan sumame kan masu sayar da motocin a yunkurinta na gudanar da bincike na tantance motocin da suke zargin ana satar shiga kasar da su ba bisa ka'ida ba.