Ana ci gaba da zanga-zanga a Masar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Masarawa na ci gaba da zanga zangar da suke yi ta kin jinin Shugaban kasar Abdul Fattah al-Sisi wacce aka fara tun a ranar Juma'a.

Sama da masu zanga-zanga 200 ne suka mamaye titunan garin Suez inda suke kira da shugaban ya yi murabus.

An shaida cewa gwamman mutane ne 'yan sandan kasar suka kama wasu kuma suka sha hayaki mai sa hawaye.

Hakazalika an gudanar da zanga-zangar a dandalin Tahrir da ke birnin Cairo a ranar Juma'a inda masu zanga-zangar ke zargin gwamnatin al-Sisi da cin hanci da rashawa.

Sai dai Mista Sisi ya yi watsi da zarge-zargen inda ya ce karya ce zalla da neman cin mutuncinsa.

Me ke faruwa ne a kasar Masar?

Tun a ranar juma'a ne 'yan kasar suka fara wallafa wasu kalamai a shafin Twitter, "Sisi ka sauka daga mukami" da "Jama'a na son hambarar da wannan mulkin", wadannan su ne kalaman da ke cin kasuwa tun da safe a kasar Masar.

Masu boren sun yi fitar dango, tare da cika dandalin Tahrir, duk kuwa da cewa an yi ta amfani da hayaki mai sa hawaye dan tarwatsa su.

Wakilin BBC a Masar ya wallafa a shafinsa na Twitter, kwanaki kadan da suka gabata idan aka ce hakan za ta faru ba lallai ne a yadda ba.

Kafar yada labaran Al Jazeera, ta rawaito zanga-zanga irin wannan ta barke a birni na biyu mafi girma a kasar wato Al-askandariyya.

A ranar 2 ga watannan ne Mista Ali da ke gudun hijira a kasar Spain, ya fara wallafa Bidiyon sukar gwamnatin Masar. A wani bidiyon da ya wallafa a ranar Talata, Mista Ali ya ce idan zuwa ranar alhamis shugaba al-Sisis bai sauka daga mukami ba, to 'yan kasar za su fito zanga-zanga dandalin Taharir a ranar juma'a.

A shekarar 2013 ne, Abdel Fattah al-Sisi ya jagoranci sojin Masar suka hambarar da gwamnatin shugaba na farko da aka zaba a tsarin dimukradiyya marigayi Muhammad morsi, bayan zanga-zangar kin mulkinsa.

Tun daga lokacin kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargin gwamnati da take hakkin jama'a, da kame dubban 'yan adawa ciki har da tsare marigayi Morsi wanda a shekarar nan ya rasu a kotu a ranar da ake zaman sauraron karar da ake masa.

A kuma watan Afirilu ne aka kada kuri'ar amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin Masar garanbawul, inda ya bai wa shugaba Abdel Fattah al-Sisi damar zama shugaban kasar har zuwa shekarar 2030.