Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Na baro Afirka ta Kudu babu ko taro'
Jirgin da ya dauko kashi na biyu na 'yan Najeriya daga Afirka ta Kudu ya sauka a birnin Legas a ranar Laraba.
Sama da 'yan Najeriya 300 cikin guda 600 da suka amince su koma gida ne jirgin ya sauke, biyo bayan munanan hare-haren da ake kai wa baki 'yan Afirka a biranen kasar.
Tun a ranar Talata ya kamata jirgin ya kwaso mutanen, amma hakan ba ta samu ba sakamakon rashin amincewa jirgin Airpeace sauka a filin jirgin sama na birnin Johannersburg.
Ko a makon da ya gabata kusan mutane 200 ne suka iso Najeriya, duk da cewa babu dan kasar ko daya daga cikin mutane 12 da suka mutu sakamakon hare-haren da ake kai wa 'yan kasashen wajen amma 'yan kasuwa sun tafka hasara.
Yawancin wadanda suka dawo gida, sun bayyana irin halin tashin hankali, da dimuwar da suka fuskanta a lokacin da suke Afirka ta Kudu, wasu daga cikinsu ba su tsira da komai ba.
Wani dan kasuwa mai suna Lucky Ekente ya shaida wa BBC irin halin da ya samu kan sa a ciki:
Yace "an kona baki dayan gidan casu da na ke da shi. Don haka na dawo Najeriya babu ko taro, sun kwashe duk abin da na mallaka."
Ya kuma godewa mai kamfanin jirgin sama na Air Peace da ya yi jigilar dauko su a kyauta ba tare da sun biya ko kwabo ba.
Sai dai Lucky ya ce ya yi matukar farin ciki da ya dawo gida a raye cikin koshin lafiya.
A hukumance sai a farkon wannan makon ne gwamnatin Afirka ta Kudu ta nemi afuwar Najeriya kan tashin hankalin da ya faru.
Najeriya da Afirka ta Kudu su ne manyan kasashe mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kuma sun amince su yi aiki kafada da kafada domin gyara dangantakar da ke tsakaninsu.