Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Najeriya na mayar da martani kan kamfanonin South Africa
A Nijeriya, wasu mutane sun kai hari wanda ga alama na ramuwar gayya ne a kan wuraren kasuwancin 'yan Afirka ta kudu da ke birnin Ikko.
Shaidu sun fada wa BBC cewa an barnata wani babban kantin saye da sayarwa na 'yan Afirka ta kudu da ke Lekki.
Haka kuma wani shaida ya ba da rahoton ganin mutum biyu a kwance kusa da kan titi a wajen shagon.
Haka zalika an lalata motocin da suka makale a cunkoson ababen hawa da ke kusa, yayin da fasinjoji ke tserewa.
Kawo yanzu hukumomi a Najeriya ba su tabbatar da rahoton samun wani da ya jikkata ko ya rasu ba.
Gwamnatin kasar ta yi kira ga 'yan Nijeriya su guji kai hari a kan wuraren kasuwancin Afirka ta Kudu.
Wane hali 'yan kasashen waje ke ciki a Afirka ta Kudu?
A kan wannan al'amari, BBC ta tuntubi wani dan Nijeriya mazaunin birnin Johanasbag na Afirka ta Kudun.
Mutumin mai suna Ibrahim Bitrus ya bayyana halin da 'yan kasashen waje ke ciki yanzu, a wata hira da yayi da BBC:
"Rikicin yaa samo asali ne a lokaicn da wani dan kasar Tanzania ya tafi wata unguwa domin sayar da wasu kwayoyi masu sa maye."
Ya ce, "Kwayoyi ne da matasa kan nuka, su saka cikin taba sauna sha. To wasu direbobin motocin tasi a unguwar sun hana yaron zuwa unguwar, amma ya ki".
"To da suka kama shi ne sai k=suka dake shi. Shi kuma sai ya tafi gida ya dauko bindiga ya harbi wani daga cikin wadanda suka doke shi", inji Ibrahim Bitrus.
Ya kuma bayyana wa BBC cewa a sanadin haka ne aka dora wa 'yan Najeriya wannan laifin, kuma daga nan aka fara kai musu hare-hare.
Ya kuma ce wutar rikicin ta fara ne daga babban birnin kasar Pretoria, kafin daga baya ta bazu zuwa birnin Johannesburg.