Yaya sunan wannan motar a yankinku?

Asalin hoton, AFP
Har yanzu Beetle na ci gaba da cin zamani a inda wasu suka zabi su ci gaba da amfani da motar da su biya haraji mai yawa a kan sabbin motoci sama da shekara 40 bayan motar ta fara tashe a kasar.
Volkswagen Beetle na daga cikin motoci masu tarihi. A baya wannan motar ta yi tashe a matsayin abin hawa na kece-raini, daidai da zamani.
Yaya ake kiran wannan motar a inda kuke?
Karbuwar wadannan motoci a kasar Habasha, na da dadadden tarihi.
Tun zamanin Sarkin-Sarakuna Haile Selassie, motoci suka samu karbuwa a kasar.
Shekara 40 bayan hambarar da mulkin Haile Selassie, har yanzu motocin na nan kamar ruwan dare a titunan kasar.
Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaitio cewa yanzu 'yan kasar sun gwammace su ci gaba da amfani da Beetle din, wadanda yanzu suke kawatawa daidai da zamani saboda yawan harajin da gwamnatin kasar ke karba a kan sabbin motoci.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, AFP
A farkon 2019, kamfanin Volkswagen ya sanar da shirinsa na bude masana'antar kera motocinsa a Habasha - amma ba zai kera samfurin Beetle ba, in ji AFP.
Volkswagen sun dakatar da kera Beetle a watan Yuli bayan sun kwashe shekara 80 suna kerawa.
Beetle ta karshe da kamfanin ya kera ita ce "Beetle Final Edition" da aka kera a Mexico.

Asalin hoton, AFP
Robel Wold mazaunin birnin Addis Ababa, ya ce daina kera motocin ya sa darajar Beetle dinsa kirar 1967 ta karu.
''Idan har an daina kera Beetle, to shi kenan muna da kadarori masu tsada.
''Za su zama kayan tarihi kuma ina ganin na yi dace. Ko an taya motata da tsada ba zan sayar ba.''











