Kotu ta yi watsi da karar Atiku Abubakar

An wallafa

Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Alkalan kotun biyar karkashin jagorancin mai shari'a Muhammad Garba ta tabbatar da Shugaba Buhari na jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben watan Fabrairun 2019.

Kotun ta yi watsi da ikirarin Atiku da PDP cewa su ne suka samu mafi yawan kuri'u a zaben shugaban kasa na 2019, bisa sakamakon da suka tattara daga rumbun tattara sakamako na intanet.

Mai Shari'a Muhammed Garba ya ce a dokar zaben Najeriya "ana aikewa da sakamakon zabe ne kawai a fili ba ta intanet ba a kowane mataki tun daga jiha har zuwa kasa baki daya".

Ya kara da cewa: "Babu wata doka da ta bai wa INEC ko wani jami'i damar tura sakamakon zabe ta intanet. Sannan kuma babu dokar da ta bai wa INEC damar yin amfani da na'urar Card Reader wurin tattara sakamakon zabe."

Sakamakon da hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar ya nuna cewa Shugaba Buhari, mai shekara 76, ya samu kuri'a miliyan 15 da dubu 200 yayin da Alhaji Atiku Abubakar, mai shekara 72, na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a miliyan 11 da dubu 300.

Zuwa yanzu ba a samu martani ba daga Atiuku Abubakar ko jam'iyyar PDP game da hukuncin kotun.

Sai dai jam'iyyarsa ta PDP ta ce za ta daukaka kara zuwa kotun koli.