Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An nada sabbin ministoci a sabuwar gwamnatin Sudan
Sabon Firai ministan Sudan Abdalla Hamduk ya bayyana ministoci 18 da za su mulki kasar, a karon farko tun bayan da aka kulla yarjejeniyar karba-karba tsakanin fararen hula da sojojin kas
Cikin ministocin akwai Asma Abdallah, mace ta farko da za ta rike mukamin ministar harkokin waje, amma sojoji ne za su rike ma'aikatun tsaro da na harkokin cikin gida.
Firai ministan Sudan Abdalla Hamdok ke nan ke cewa yana da karfin gwuiwa cewa gwamnatin da zai jagoranta za ta iya shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.
An dai samar da wannan gwamnatin ne a dalilin yarjejeniyar raba mukamai da sojojin kasar suka kulla da fararen hula masu zanga-zangar neman tabbatar da mulkin demkradiyya.
Firai minista Abdalla Hamdok ya bayyana sunayen ministoci 18 da za su kama aiki tare da shi a sabuwar majalisar ministoci, sannan ya ce zai bayyana suna wasu mutum biyu daga baya.
Ya yi alkawarin jagorantar gwamnatin da za ta gudanar da ayyuka dominci gaban kasar, kuma ya ce akwai garambawul da ya zama wajibi a yi wa tsarin kasar.
Firai minista Abdalla Hamdok ya ce: "A yau kasarmu za ta shiga wani sabon babi, babin da idan muka tafiyar da shi bisa tsari, za mu gina kasar Sudan da za mu yi alfahari da ita. Kasar da ke mutunta bambance bambance, za mu samar da kasar Sudan wadda ke bin tafarkin demokradiyya domin amfanin kowa."
Gwamnatin hadaka
Yawancin ministocin da aka bayyana sunayensu jiya Alhamis sun fito ne daga bangarori biyu - na sojojin kasar da bangaren gamayyar kungiyoyin fararen hula masu rajin kawo sauyi a kasar.
A cikinsu akwai Asma Abdallah, wadda ita ce za ta zama mace ta farko da za ta rike mukamin ministar harkokin waje a kasar.
Sai kuma Ibrahim Elbadawi, wani kwararren masanin tattalin arziki wanda zai rike mukamin ministan kudi, da Madani Abbas Madani, wanda shi ne jagoran hadakar kungiyoyin fararen hula da suka tattauna da majalisar mulkin soja ta kasar har aka kulla yarjejeinyar rabon mukamai.
A bangaren sojoji kuwa, Janar Jamal Omar - wanda mamaba ne na majalisar mulkin soja - shi ne zai zama ministan tsaro.
Cikin manyan kalubalen da ke gaban wannan gwamnati Firai minista Abdalla Hamdok shi ne na samo kudaden da za a ci gaba da shigo da kayayyakin abinci da 'yan kasar ke bukata matuka.ar.