An cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka a Sudan

An wallafa

Mukarraban gwamnatin soji da wakilan gamayyar jam'iyyu masu hamayya na Sudan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka, a yayin wani biki da aka gudanar ranar Asabar a Khartoum, babban birnin kasar.

Yarjejeniyar dai za ta bude wani sabon babin gwamnati a kasar da za ta kunshi sojoji da kuma farar hula gabanin gudanar da babban zaben da zai mayar da kasar turbar mulkin dimokradiyya.

Hemeti da Laftanar Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ne suka wakilci gwamnatin soji ta wucin gadi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar, inda kuma Ahmed al-Rabie ya wakilci gamayyar kungiyoyin Alliance for Freedom and Change masu son ganin Sudan ta koma turbar dimokradiyya.

Karkashin yarjejeniyar, za a samu majalisa mai cikakken 'yanci da ta kunshi farar hula guda shida da janar-janar na soja guda biyar domin tafiyar da al'amuran mulkin kasar na shekaru fiye da uku lokacin da za a gudanar da babban zabe.

Bangarorin biyu sun amince su yi karba-karba na ikon majalisar har tsawon shekaru uku. A mako mai zuwa ne kuma za a sanar da sabon firaiministan da al'ummar kasar suka zaba.

Ana dai sa ran wannan yarjejeniyar za ta kawo karshen kiki-kakar da kasar ta kwashe watanni tana fama.

Shugabannin kasashen Ethiopia da Egypt da Sudan ta Kudu na daga cikin shugabannin nahiyar Afirka da suka halarci bikin cinmma wannan yarjejeniya.

Mohamed Hamdan "Hemeti" Dagolo - wanda aka fi sani da 'mutumin da ya fi kowa karfin fada a ji a Sudan' ya yi alkawarin bin yarjejeniyar sau da kafa.

Abin da ya faru a Sudan

Za a iya alakanta rikicin da Sudan ta yi fama da shi da matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin tsohon shugaba Omar El-Bashir ta dauka a watan Disamban 2018.

A lokacin ne gwamnati ta rage tallafin da take bai wa biredi da man fetur, al'amarin da ya haifar da tsadar rayuwa, inda jama'ar yankin gabashin kasar suka fusata suka fara gudanar da jerin zanga-zanga.

Daga bisani zanga-zangar ta karade birane da dama da suka hada da Khartoum babban birnin kasar.

Zanga-zanagr neman saukin rayuwa ta rikide daga bisani zuwa ta bukatar Shugaba Omar El-Bashir wanda ya kwashe shekaru fiye da 30 yana kan karaga, da ya yi murabus.

A watan Afrilu ne kuma sojoji suka hambarar da Shugaba Omar El-Bashir din sakamakon wani zaman dirshan da 'yan kasar suka yi a wajen ginin ma'aikatar tsaro ta kasar suna neman taimakon sojoji wajen tunbuke shugaban.

To sai dai jim kadan bayan hambarar da El-Bashir, sai 'yan kasa suka nemi da a mika mulki ga farar hula ba soji ba.

Majalisar sojoji da Laftanar Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ya jagoranta ta yi iya bakin kokarin ganin kura ta lafa amma al'amari ya ci tura.

Sojoji ba su kadai ne ke da karfi ba a Sudan kasancewar akwai kungiyoyin tsaro da ba na soji ba da na mayakan sa-kai musulmi da suke da karfin iko.