Xenophobia: Najeriya ta aike wa jakadan Afrika Ta Kudu sammaci

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Najeriya ta aike wa jakadan Afirka ta Kudu a kasar sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar.

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama zai gana da jakadan Afirka Ta Kudu a ranar Talata kan kashe-kashe na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

Ya kuma ce dole Afirka Ta Kudu ta biya 'yan Najeriya diyyar asarar da aka jawo musu.

Onyeama ya wallafa wani sako a Twitter ranar Litinin yana mai cewa tura ta kai bango, dole kuma Najeriya ta dauki mataki a wannan karon.

'Yan Najeriya da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu tare da yin kira ga gwamnati da ta dauki matakin dakatar da kashe-kashen.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani kan wannan labari.

'Kar ku sa kayan kawa masu tsada'

Ofishin jakadancin Habasha a Afirka Ta Kudu ta shawarci jama'ar kasarta da su rufe harkokin kasuwancinsu yayin da ake tashin hankalin, a cewar kafar yada labaran kasar.

Kafar yada labaran ta kuma ce Habashan ta shawarci mutanenta da cewa su nesanta kansu daga duk wani fito-na-fito da kuma rikici, kar kuma su sanya kayan kawa masu tsada a lokacin da za su fita.

A wasu wuraren, 'yan sanda sun yi kokarin dakatar da sace-sace.

A hannu guda kuma, ministan sufuri na Zambiya ya ce masu manyan motoci su guji zuwa Afirka Ta Kudu har sai harkar tsaro ta inganta.

An fadi sanarwar ce sakamakon hare-haren da aka kai wa motocin dakon kayan na kasashe makwabta.

Wata kafar yada labaran Afirka Ta Kudu IOL ta ce, an samu rahotannin cewa an tsare manyan motoci da dama tare da yi musu sace-sace.

Ministan 'yan sanda na Afirka Ta Kudu, Bheki Cele, ya ce "fashi da makami ne ya jawo rikicin ba wai kin jinin baki ba."

Ya shaida wa manema labarai cewa ana amfani da kalmar kin jinin baki ne kawai don a sakaya zancen. "Babu wani abu da ya jawo tashin hankali tsakanin 'yan kasar da baki," in ji shi.

Cyril Ramaphosa ya mayar da martani

A wani bangaren kuma, Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda 'yan kasarsa ke kai hari ga shaguna da kuma wuraren kasuwanci na baki mazauna kasar.

Mista Ramaphosa ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya saka a shafinsa na Twitter inda ya ce 'yan kasar tasa ba su da ikon kai hari ga wani bako a tsarin doka.

Ya kuma bayyana cewa zai yi taro na musamman kan tsaro da ministocinsa da kuma domin ganin yadda za a shawo kan matsalar.

Ya kuma bukaci shugaban 'yan sandan kasar da ya ziyarci wuraren da aka fi samun rikice-rikicen a kasar domin tabbatar da tsaro.