Wata gamayyar kungiyoyin Arewa ta ce za ta dauki mataki kan raina 'yan Arewa

Legas ne cibiyar kasuwanci ta Najeriya

Asalin hoton, FACEBOOK/LAGOS STATE GOVERNMENT

An wallafa

Al'ummar yankin Arewacin Najeriya na ci gaba guna-guni kan wani mataki da gwamnatin jihar Legas a kudu-maso-yammacin kasar ta dauka na tsare wasu matasa `yan jihar Jigawa da suka je ci-rani a jihar.

Wannan lamari dai ya fusata shugabannin al'ummar arewacin Najeriyar, duk kuwa da cewa mahukuntan jihar Legas sun saki matasan, bayan gudanar da bincike.

A ranar Juma'a hukumomi a Legas din sun tsare wasu matasa 123 wadanda suka fito daga Arewacin Najeriya inda suka bayyana su a matsayin barazana ga tsaron birnin.

Sai dai bayan kwana guda an saki matasan bayan da jami'an tsaro suka ce sun gane cewa 'yan Najeriya ne kuma ba su aikata wani laifi ba.

Amma gamayyar kungiyoyin al`ummar arewacin Najeriya ta bayyana matakin da cewa cin zarafi ne, kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Ashiru Sharif shi ne shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin, ya shaida wa BBC cewa gazawar shugabanni wajen kare hakkin `yan arewacin kasar ce ke ja wa 'yan arewa wulakanci.

Ya ce "Da suka binciki mutanen nan ba su kama su da laifi ba, mene ne dalilin tozartar da su a jera su a layi ana daukan hotonsu ana maganganu?"

Kungiyar ta nuna cewa tafiyar mutanen a cikin kungiya manuniya ce kan cewa ba su da wata mummunar nufi a tattare da su.

Ashiru Sheriff ya ce a yanzu za su dauki mataki, za su bukaci a dawo da duk wasu damammaki da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa al'ummar Arewa, wadanda aka danne.

Wadannan damammaki sun hada da kason guraben ayyukan yi da ake bai wa al'ummar wurin da aka kafa kowane kamfani.

Ya ce za su tabbatar an yi doka a dukkanin jihohi 19 na Arewacin kasar wadda za ta tabbatar da cewa ana bai wa 'yan asalin jihar da aka kafa kowane kamfani kaso 70 cikin 100 na ma'aikatan da za a dauka.

Hakan a cewarsa zai samar da ayyukan yi ga matasa, sannan ya fitar da su daga dabi'ar shan miyagun kwayoyi da dabanci.

Yawan al'umma a Legas na karuwa sosai

Legas ne tsohon babban birnin Najeriya, kuma nan ne cibiyar kasuwanci ta kasar.

Mutane daga kowane bangare na kasar kan yi tururuwa zuwa birnin domin neman sana'a.

Majalisar dinkin duniya ta ce al'ummar jihar Legas sun kai miliyan 14, sai dai gwamnatin jihar na ganin cewa sun kai miliyan 21.