Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce matsayar INEC bayan da kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye?
Kotun sauraron kararrakin zabe ta garin Lokoja da ke jihar Kogi ce ta soke zaben Sanata Dino Melaye, wanda yake wakiltar shiyyar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.
Yayin zaman kotun na ranar Juma'a ne aka soke zaben kuma aka umarci sake sabon zabe a shiyyar.
To amma mece ce matsayar hukumar zabe game da wannan hukunci?
Mai magana da yawun hukumar zabe a Najeriya Aliyu Bello ya shaida wa BBC cewa ya zuwa lokacin da aka tattauna da shi hukumar zaben Najeriya INEC ba ta samu hukuncin kotun ba.
Sannan kuma ya ce ko da an mika wa hukumar ta INEC hukuncin, Dino Melaye na da ikon daukaka kara a cikin kwana 21.
Ya ce idan Sanatan ya daukaka kara to dole a jira sai kotun da zai je din ta yanke hukunci kafin a san wane mataki za a dauka.
Bayan yanke wannan hukuncin Sanata Melaye ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce zai daukaka kara zuwa gaba, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Sanata Melaye ya fara zama dan majalisar wakilan kasar ne a shekarar 2007, inda yake wakiltar mazabar Kabba da Ijumu da ke jihar Kogi.
Sai da ya yi wa'adi biyu a majalisar wakilai kafin ya lashe zaben dan majalisar dattawa a shekarar 2015.
Kazalika a watan Yuni ne ya bayyana muradinsa na shiga takarar neman gwamnan jihar Kogi, wanda za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.
Har ila yau, Sanata Melaye ya ce wannan hukunci ba zai sa shi ya raba hankalinsa ba dangane da aniyyarsa ta neman zama gwamnan jihar ba, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.