Soja ne zai jagoranci gwamnatin hadaka a Sudan

Lt-Gen Abdel Fattah Abdelrahman Burhan - Janar Abel Fattah Abdelrahman Burhan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Janar Burhan ne zai jagoranci gwamnatin hadaka a watanni 21 na farko
An wallafa

An rantsar da shugaban gwamnatin hadaka a Sudan, Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a matsayin sabon shugaban gwamnatin da aka kafa.

Zai jagoranci wata tawagar fararen hula shida da kuma jami'an soji hudu a yayin mayar da mulkin kasar zuwa tafarkin demokradiyya wanda aka kiyasta cewa zai kai tsawon watanni 39.

Wannan sabuwar gwamnatin dai na zuwa bayan da aka hambarar da Omar al-Bashir a cikin watan Afrilun da ya gabata.

Ya shafe shekara 30 yana mulkin kasar amma jami'an soji sun hambarar da shi bayan da aka shafe watanni ana zanga-zanga.

A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnatin hadakar da shugabanin fararen hula suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar da za ta bude babin tafarkin demokradiyya a Sudan.

Janar Burhan ne zai jagoranci gwamnatin a farkon watanni 21, daga baya kuma fararen hula za su maye gurbinsa har sai an gudanar da zabe a shekarar 2022.

Za a rantsar da saura mambobi 10 a ranar Laraba, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Za a kuma rantsar da sanannen masanin tattalin arziki Abdalla Hamdok wanda jagoran zanga-zangar fararen hula suka zaba a matsayin firai minista.

Rundunar sojin kasar kuwa za ta zabi ministocin harkokin tsaro da na cikin gida wadanda za su kasance a cikin gwamnatin.

Wacce yarjejeniya bangarorin biyu suka kulla?

A ranar 4 ga watan Agusta rundunar soji da masu zanga-zanga suka saka hannu kan wata yarjejeniyar domin samar da gwamnatin rikon kwarya.

An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 17 ga watan Agusta.

Wasu mata kenan lokacin da suke nuna farin cikinsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane sun yi murna a ranar 4 ga watan Agusta lokacin da aka saka hannu kan yarjejeniyar