'Yan ciranin Syria na tsaka mai wuya a Turkiyya

Asalin hoton, AFP
An bai wa dubban 'yan ciranin Syria zuwa ranar Talata da su bar birnin Santanbul na kasar Turkiyya ko kuma a kore su daga kasar.
Hukumomi sun umarci 'yan ci ranin da ba su da takardar shaidar zama da su koma yankin da aka yi musu takardar. Hakan dai wani yunkuri ne na rage mutane a birnin.
Amma wasu 'yan Syria sun bayyana wa BBC cewa an fara tasa keyar mutane zuwa Idlib, inda ake fama da rikice-rikice cikin Syria.
Sun ce ana tilasta wa mutane saka hannu kan wasu takardun da ba za su iya karantawa ba ko kuma su fahimta ba.
An dai yanke hukuncin korar ne a karshen watan Yuli, lamarin da ya bai wa wadanda abin ya shafa akalla wata daya su aiwatar da abin da ake bukata da su.
Tun da aka fara yakin basasa a Syria cikin shekaru takwas da suka gabata, fiye da 'yan Syria milliyan uku da dubu dari shida sun gudu zuwa makwabciyar kasarsu Turkiyya a cewar wakilin BBC, Mark Lowen.
A kalla mutum 500,000 ne suka yi rajista a Santanbul - amma an kiyasta cewa mutum miliyan daya ne ke zaune a yankin, wadanda suka taho daga wasu yankuna daban da suka fara yin rajista.
Lokacin da ya ke bayyana hukuncin a cikin watan da ya gabata, gwamnan Santanbul ya umarci 'yan Syria da ke da ikon zama a birnin da su rinka yawo da takardunsu da kuma fasfunansu a kowane lokaci.
Ya kuma ce za aci gaba da gudanar da bincike a wuraren da ake shiga ababen hawa.
A farkon watan Augusta, an mayar da 'yan cirani 12,000 zuwa yankunansu da suka yi rajista, kuma an saka fiye da mutum 2,600 da ba su yi rajista ba cikin cibiyoyin da ke karkashin kulawaR ministan harkokin cikin gida.
An binciki dubban wuraren aikin domin kauce wa daukar ma'aikatan da ba su da rajista.
Gwamnatin Turkiyya ta ce za a kai dukannin 'yan ciranin da ke son su koma Syria zuwa wurare da ke wajen kasar masu tsaro wadanda ke karkashin ikon rundunar sojin Turkiyya.
Amma BBC ta yi magana da 'yan Syria wadanda suka ce motocin bas-bas da ke daukar 'yan Syria suna kai mutane zuwa yankin Idlib - a dai-dai wajen iyaka wurin da ake yawan rikice-rikice.
A ranar Litinin, wani harin saman da gwmnatin Syria ta kai kan wani jerin gwanon motoci ya kashe a kalla fararen hula uku tare da kuma raunata mutum 12, a cewar Turkiyya.
An yi tunanin cewa wata yarjejeniyar da aka cimma a cikin shekarar da ta gabata za ta kara kawo zaman lafiya a yankin, amma gwamnatin ta Syria ta ci gaba da kai hare-hare a cikin watannin da suka gabata.










