Tunde Fowler: Dalilan da gwamnatin Jonathan ta fi samun kudin shiga

Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya
An wallafa

Shugaban hukumar tara haraji ta Najeriya FIRS, Tunde Fowler ya amsa tambayoyin da ofishin shugaban yayi masa kan raguwar kudaden haraji a kasar.

A cikin takardar da ya aika wa Abba Kyari, wanda shi ne shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya, Mista Fowler ya amince cewa adadin harajin da hukumarsa ta tara bai kai yawan wanda aka samu ba karkashin gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Johnathan.

Amma ya ce hukumar ta yi gagarumin kokarin wajen tara wasu jerin haraji kamar VAT da CIT.

Mista Fowler ya bayana cewa baban dalilin da ya sa hukumar tara haraji ta najeriya ba ta iya tara karin haraji tun 2015 shi ne koma bayan tatalin arzikin da kasar ke fuskanta dangane da kasuwar man fetur ta duniya.

Ya ce wannan matsalar ce ta janyo raguwar hada-hadar kasuwanci a fadin kasar.

Ya kuma bayyana cewa bangarori biyu na kudaden shiga da Najeriya ke samu su ne na man fetur, wanda shi ne ke kan gaba - da sauran kasuwanci da bai shafi man fetur ba.

Pound sterling

Asalin hoton, Getty Images

Alkaluman da ya nuna na cewa tsakanin shekarun 2012 zuwa 2016, adadin kudaden shiga da Najeriya ta samu sun kai tiriliya 12, da miliyan 190.

Amma Najeriya ta sami tiriliyan 16 da biliyan 771 ne tsakanin 2016 zuwa 2018, wanda kari kashi kusan 38 cikin 100 ne.

Ya kuma nuna cewa bangaren mai ne ya kashi 57 cikin 100,, inda bangaren da ba na mai ba ke da kashi kusan kashi 43 cikin 100.

Ya kuma kare hukumarsa, inda ya ce tana da iko ne kawai kan angaren da ba na mai ba, wanda shi ya sami karuwa sosai.

Yadda lamarin ya samo asali

Kamar yadda wasikar da ofishin shiugaban Najeriya wadda ta bukaci Mista Fowler ya bayyana dalla-dalla dukkan dalilan da suka janyo koma bayan da kasar ke fuskanta, shugaban hukumar ta tara haraji ya nuna wasu alkaluma da ke nuna dukkan sassan da kasar ke amfani da su wajen tara haraji,

Kuma ya kwatanta adadin kudaden bangare da ba na mai ne ba da hukumar ta tara a shekarun 2012 - 2014 da na shekarun 206 zuwa 2018.

Alkaluman sun nuna cewa an sami karuwa a kusan dukkan sassan, wadanda suka hada da kudaden harajin ma'aikata da na kayayyaki wato VAT da harajin da kamfanoni ke biya wato Corporate Income Tax.

A karshe wasikar ta Mista Fowler ta bayyana dalilai biyu da suka janyo koma bayan da Najeriya ke fuskanta wajen tara haraji a bangaren man fetur - inda ya ce na farko shi ne faduwar farashin man a kasuwar duniya musamman a shekarun 2015 zuwa 2017.

Dalili na biyu shi ne koma bayan tatalin arziki da Najeriya ta fuskanta a daidai wannan lokacin, wanda yanzu ne ta ke farfadowa daga matslolin da koma bayan ya haifar.