Tsaka mai wuya: Danta za ta bi na mayakin IS ko 'ya'yanta na kabilarta?

- Marubuci, Daga Nafiseh Kohnavard
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Fasha
- An wallafa
Gashin kan Adam ruwan gwal ne kuma idanunsa kore ne. Ba kamar 'yan uwansa ba.
"A tun lolacin da na ji kukansa na farko bayan haihuwarsa na ji ina matukar kaunarsa," in ji mahaifiyarsa Jovan.
Haske ne shi a cikin duhu. Sai dai mahaifin Adam shi ne mutumin da ya kama ta a matsayin baiwa. Amma a yanzu dole ta hakura ta bayar da Adam.
Jovan na son rayuwarta da kuma son zama da mijinta a kyakkyawan kauyen da suka taso a ciki.
Ba ma lokacin da ta fi so irin da dare a lokutan bazara, da shan shayi a kan rufin gidansu tare da mijinta Khedr.
Suna zare jiki su hau kan rufin ne da zarar yaransu sun yi bacci. A lokacin sama kan yi haske tarwal ta kuma cika da taurari.
Jovan ta ce, "Na kasance cikin farin ciki, na yi rayuwa mafi dadi."
Amma rayuwarta ta sauya ne har abada a lokacin bazarar 2014.
Wata rana a farkon watan Agusta, jim kadan bayan cin abincin rana, sai wasu motoci masu dauke da bakaken tutoci suka iso kauyen.

Asalin hoton, Getty Images
Jovan da Khedr ba su tabbatar da abin da ke faruwa ba amma sun san cewa za su iya fadawa hadari.
A bayyane yake karara cewa mutanen da suka zo din 'yan kungiyar IS ne.
Amma kuma wasu daga cikin mutanen ba boyayyu ba ne - 'yan wani kauye ne da ke kusa da nasu kuma Khedr ya san su.
Mutanen sun yi alkawarin cewa ba za su cutar da kowa ba idan dai sun bayar da hadin kai.
An tursasawa iyalan tare da wasu iyalan 20 tafiya a tawagar 'yan IS din daga wani kauyen zuwa wani a tsaunin Sinjar.
Abin da ma'auratan ba su fahimta ba shi ne wannan hari ne da aka shirya daga sansanonin IS da ke Iraki da Syria.
A farkon shekarar, kungiyar ta kame wasu birane a kusa da Bagadaza.
Bayan wata biyar aka kwace birnin Mosul, wanda ke kusa da kauyen su Jovan da Khedr. A yanzu ma IS ta zo da irin wannan burin.
Nan da nan labarin ya bazu a tsaunin kuma a yayin da ayarin ya isa inda za a yada zango bayan sun ci rabin tafiya, 'yan kauyen da dama sai suka tsere can saman tsaunin Sinjar.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana watan Agustan 2014 a matsayin wanda aka fatattaki kungiyar IS daga arewacin Iraki, sannan kuma a lokacin IS din ta fiddo da wani sabon salon mafi muni.
Jagiran tawagar ya umarci Khedr cewa ya hau tsaunukan da shawo kan mutanen kauyukan su dawo - ba su da niyyar cutar da su.

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin wadanda suka gudu kan tsaunukan ma kaninsa ne. Khedr ya so ya koma wajen iyalinsa amma sai kaninsa ya ce yin hakan tamkar sayar da rai ne.
An san mayakan IS da yin dauki daidai ga mutanen da suka ga ba za su yi musu amfani ba, sai su kashe su. Kamar matarsa, shi ma Khedr yana cikin kabilar Yazidi da ke fuskantar barazana.
'Yan kabilar ta Yazidi ba su da wani zabi. Wadanda suka tsere zuwa tsaunin Sinjar sun shiga tarko.
Babu ruwa babu hanyar samunsa, daruruwan mutane sun mutu saboda tsananin zafin da ya haura maki 50 ma'aunin salshiyas.
IS ta kama sauran dubban mutanen da ba su samu hawa tsaunukan ba.
An raba iyalai - an tilastawa yara maza koyon atisaye a sansanonin IS, su kuwa yara mata da manyan mata aka mayar da su tamkar bayi inda ake kwanciya da su.
Maza kuwa da suka ki karbar Musulunci sai aka kashe su.
Babu wanda yake da tabbas kan ko 'yan kabilar Yazidi nawa IS ta kama.
Wani wakilin MDD na musamman ya kiyasta cewa 'yan Yazidi 400,000 ne ke zaune a Sinjar a lokacin, an kashe dubbai sannan an mayar da kusan 6,400 bayi inda aka yi ta musu fyade da azabtar da su da dukan su da kuma sayar da su, musamman mata daga cikin su.
An sa Jovan da 'ya'yanta uku da kuma wasu matan kusan 50 a cikin wata babbar mota.
A karshe aka tafi da su garin Raqqa da ke Syria - wanda a wancan lokacin can ne hedikwatar daular IS.
Jovan ta ce "ba abin da za mu iya yi don kare kawunanmu." Ba za ta sake ganin Khedr ba har sai bayan wasu shekarun hudu.
Kangin bauta

Nan da nan Jovan ta fahimci cewa inda aka kai su a Raqqa kasuwar bayi ce.
An tsare ta da yaranta da wasu matan da dama da yara a wani gini mai hawa uku - dukkansu dai sun kai kusan mutum 1,5000.
Jovan ta ce ta san da yawan matan - yawanci 'yan uwa ne sai kuma makwabta daga kauyuka daban-daban.
"Mun yi ta kokarin bai wa juna baki da fatan cewa wata mu'ujiza za ta faru a sake mu," a cewarta.
A maimakon haka ma, sai ga shi ana tursasa mata cewa dole ta zabi wanda zai zama mijinta cikin mayakan IS din.
An bayar da ita ga wani dan Tunusiya mai suna Abu Muhajir al Tunisi, wani babban kwamanda - matashi dan siriri mai dogon gemu.

Asalin hoton, Getty Images
An sa Jovan ta musulunta ta kuma aure shi.
Ta shafe kwanaki tana kuka. Ta yi kokarin guduwa sau uku amma ba ta yi nasara ba, sannan kuma yaranta na jawo tsaiko wajen hakan - babban shi ne Haitham, wanda ke da shekara 13 a lokacin, amma karamin Azad, yana da shekara uku.
Duk lokacin da aka gano kokarinta na guduwa Abu Muhajir kan rufe ta a daki.
"Na yi tunanin kashe kaina zai fi mun sauki, amma kuma sai na tuna da yarana. Me zai faru da su idan na bar su?"
A karshe dai Jovan ta ga ba ta da mafita sai ta karbar musulunci.
Har yanzu Jovan na cikin kaduwa ta yadda ba ta iya bayani sosai kan wanda ya sace ta.
Sai dai kuma ta ce abin mamakin shi ne ya bar ta ta zauna da 'ya'yanta har ma ya yi alkawarin kulawa da su.
An raba yara da dama 'yan kabilar Yazidi da iyayensu - an kai yara mazan sansanin koyon yaki, matan kuma aka mayar da su bayi ana kwanciya da su tare da sanya su ayyukan dida.
Jovan da 'ya'yanta da wannan dan Tunusiyan sun koma wani gida a Raqqa wanda mazauna cikinsa suka tsere.
Zuwa wannan lokacin IS na da ikon mafi yawan yankuna a Iraki da Syria - wani yanki da cibiyar yaki da ta'addanci ta Amurka ta ce ya kai girman Birtaniya.

A duk lokacin da bai tafi filin daga ba, dan Tunusiya kan kula sosai da 'ya'yan Jovan kamar yadda ya yi alkawari, don har filin wasa ya kan kai su.
Sai dai wani tashin hankalin da Jovan ta shiga shi ne na yadda a watanni biyar na farko ta gane ta samu ciki.
"Babu magani kuma ban san me zan yi ba," in ji Jovan.
Kusan a kullum sai Gamayyar hadakar sojoji da Amurka ke jagoranta ta kai hari, kuma mayakan Iraki da na Kurdawa na ci gaba da fafatawa a wurare daban-daban a Syria da Iraki.
Dan Tunusiyan da ke rike da Jovan kan shafe lokaci mai tsawo a filin daga ta yadda har ya yanke shawarar sayar da ita ga wani mayakin IS din.
Haka ake yawan sayar da 'yan kabilar Yazidi daga nan zuwa can. Amma da ya gane tana da ciki sai ya sauya ra'ayinsa.
A lokacin da cikinta ya shiga wata bakwai sai ta samu labarin an kashe Abu Muhajir a wajen yaki.
Don haka a yanzu alhakin kula da dan ya rataya a wuyanta ita kadai.
An haifi Adam a lokacin da kusan kullum sai an kai hare-haren sama a Rakka karkashin jagorancin gamayyar dakarun da Amurka ke jagoranta.
Hawa da Haitham sun taimakawa mahaifiyarsu yayin haihuwar kaninsu.. Jovan ta ce ba ta san yaya yaran suka ji da samun kani ba wanda sam bai yi kama da su ba ta ko ina.
"Ina tsammanin yarana na son sa. Sun kula da shi. Musamman ma Hawa - wacce take 'yata kuma babbar kawata.
Ta kan ba shi abinci ta yi rainonsa har sai ya yi bacci."
Yawan hare-haren da ake kai wa sun tilastawa Jovan tashi daga wannan gidan zuwa wani. Ana yawan dauke wutar lantarki. Su kan yi amfani da janareto amma idan sun samu man fetur kawai.
Samun abinci ma abu ne mai wahala, don haka Jovan ba ta ci da yawa don 'ya'yanta su samu.
"Wasu lokutan biredi kawai muke ci mu sha ruwa da sikari kadan. Na san cewa idan ban ci abinci isasshe ba, ba zan samu na shayar da Adam yadda zai gamsu ba, amma kuma ba ni da zabi."
Duk da tsananin wahalhalun da take fuskanta, ta ce ganin Adam na kara mata kwarin gwiwa.
"Yana da shiga rai. Na san cewa ba dan mijina na ainihi ba ne kuma babansa dan ta'adda ne, amma dai Adam jini da tsokata ne.
Tsira

A can Iraki kuwa, Khedr bai san komai ba game da haihuwar sabon dan da matarsa ta yi. A takaice dai bai ma san komai ba game da halin da iyalansa ke ciki.
Yanzu an kai wata 14 kenan tun bayan da aka sace su kuma ya yi ta neman su ba gajiyawa. Duk lokacin da ya ji an ce an sako wata mace da 'ya'yanta sai ya tafi kan iyaka don ganin ko iyalansa ne.
A karshe dai ya gano inda suke. Ya gano su ta hanyar wasu masu fasa kwabrin mutane da ke sayo mata da yara 'yan kabilar Yazidi daga hannun mayakan IS.
Khedr na bukatar sayen kowane dansa a kan dala 6,000. Haitham da Hawa da kuma Azad sun sake haduwa da mahaifinsu.
Sai dai ita Jovan dole ta kara tsayawa har wasu shekaru biyun a Raqqa. Ba za ta iya tabbatar da ko Khedr zai amince da Adam ba.
Khedr ya debi tsawon watanni yana cikin damuwar abin da ya kamata ya yi.
'Yan kabilar Yazidi da yawansu bai wuce miliyan daya ba a duniya sun kasance suna da tsauraran dokokin addini da al'adu.
Daya daga ciki kuwa shi ne cewa duk wanda ya bar addinin to ba zai koma ba, amma babbar hukumar addini ta Yazidi ta sassauta wannan dokar don a bai wa matan da IS ta tursasa musu damar komawa addinin.
Sai dai kuma akwai bambanci wajen daukar mataki kan yaran da aka haifa da mayakan IS.
Addininsu irin wanda sai dai a haife ka a ciki ne kawai amma ba sa karbar sabon shiga, don haka za a amince da yaro ne kawai idan iyayensa duk 'yan Yazidi ne.
A yanzu Jovan na zama ne tare da sauran mata 'yan Yazidi da aka kama wadanda duk mazajensu na IS suka mutu.
Dukkan matan na tsoron komawa kauyensu na Sinjar saboda gudun tsangwama.
"Wasun su na da fiye da da daya da mayakan IS daban-daban, don haka suna matukar tsoron komawa ga iyalansu," a cewarta.
A karshe dai Khedr ya yanke shawarar cewa lallai yaransa na bukatar mahaifiyarsu, don haka sai ya cewa Jovan yana maraba da Adam.
Jovan ta koma kauyensu Sinjar tare da Adam, wanda a yanzu ya yi wayo, bayan da ta shafe shekara hudu ba ta nan.

Amma kwanaki kadan bayan hakan sai al'amura suka sauya. Jovan ta ce sai iyalanta suka fara damunta cewa lallai sai dai ta hakura da Adam.
"Sun fara min magana a kan muhimmancin addininmu, da kuma yadda al'ummarmu ba za ta taba amincewa da dan Musulmi wanda babansa mayakin IS ne ba.
Sai Khedr ya kai Jovan wajen Sakineh Muhammed Ali Younes, mai kula da gidan marayu a Mosul.
Yana fatan ta iya shawo kan Jovan ta bar mata rikon Adam.
Sakineh ta ce ta shafe sa'o'i tana kokarin shawo kan Jovan. Ta ce Khedr ya shiga damuwa yana ta kuka.
Jovan ta kankame Adam tana cewa ba za ta iya hakura da shi ba.
Sekinah ta ce: "Hawaye ya yi ta kwarara daga idanunta a yayin da take mika yaron."
Ta ce "babu wani abu mafi muni kamar raba uwa da danta. Tamkar yanke wani sashe na zuciya ne."
"Amma bukatun al'ummar Yazidi ya fi burin mutum daya jal.
"Ni da mijinta mun amince cewa zan dauki yaron ta kowane hali. A karshe dai babu wata hanya sai ta yin karya."
Sakineh ta cewa Jovan ta bar mata Adam na 'yan makonni kawai saboda ba shi da lafiya da kuzari don haka yana bukatar a kula da shi sosai.
"Na ce mata, danki na karkashin kulawata har sai kin samu mafita a lamarin nan. A lokacin da ta rike hannuna sai da na ji tamkar wuta ce ke tashi a cikin jikinta."
Rabuwa mai ciwo

Sabuwar shekarar kabilar Yazidi ta zame wa Jovan lolaci na farko da za a yi wannan biki da ita bayan shekara hudu da ta shafe ba ta tare da iyalinta.
Sun fita sayyyar launukan da za su yi wa dafaffen kwai ado da shi kamar yadda ake yi a kabilar Yazidi.
Amma duk da cewa a yanzu tana tare da 'ya'yanta da take kauna, Jovan na cikin tashin hankali.
Kwanaki kadan bayan da ta baro gidan marayun ta yanke shawarar rungumar kaddara a yadda ta zo mata da kuma mayar da hankali kan sauran yaranta uku.
A yanzu dai tana ganin abin ba mai yiwuwa ba ne.
Ta ce "ko yaushe cikin tunaninsa nake.
"Kowane dare sai na yi mafarkinsa. Yaya za a yi na manta da shi? Ni na shayar da shi kuma dana ne. Bari na tambaye ki mana: Wai mata irin mu sun yi kuskure ne?
"Shin ba daidai ba ne mu yi kewar 'ya'yanmu?"

Asalin hoton, Getty Images
Bayan makonni da dama, Jovan ta kasa hakuri. Sai ta yanke shawarar da ta yi zaton ba gudu ba ja da baya.
Ta cewa 'ya'yanta za ta je birnin Dohuk don a duba lafiyarta saboda dimuwar da take ciki.
Amma a takaice dai gidan marayun nan ta koma.
Ta ce "ranar da na bar su ta zamo ta tashin hankali.
"Amma a gaskiya ina tunanin na ci amanar dana. Sauran yarana uku duk sun girma suna da wayo, (babban su ya kai shekara 13, sannan babansu na tare da su.)
"Amma shi Adam ba shi da kowa. Marayan yaron ba shi da kowa a duniya, kuma ina kewarsa dare da rana."
A yayin da Jovan ta isa gidan marayun sai aka shaida mata cewa Adam ba shi da lafiya don haka ba za ta iya ganinsa ba.
A karshe dai bayan kwana biyu zuwa uku sai aka sanar da Sakineh gaskiyar cewa an samu matsala a gidan marayun, al'amarin da ya jawo aka bayar da wasu daga cikin yaran ga iyalai masu son riko ta hannun wani alkali a yankin.
Sakineh ta ce ta samu alkalin ta kuma gaya masa cewa da Adam da wasu yara hudu masu irin matsayinsa da aka kai su tare bai kamata a bayar da su riko ba saboda an yi yarjejeniyar wata rana iyayensu na iya komawa daukarsu.
Amma duk da hakan dai an riga an bayar da Adam.
Sakineh ta ce Jovan ta yi kuka kamar ba gobe a lokacin da ta ba ta wannan labari.
Hakan ya sa ta kasa komawa gida sai kawai ta nemi wani sansanin 'yan gudun hijira na mata a arewacin Iraki ta zauna.
Watanni kadan bayan haka sai Khedr ya sake ta, ya kuma aika mata sako cewa ba za ta iya sake ganin 'ya'yanta ba.

Asalin hoton, Getty Images
A can kauye kuwa Khedr ya kasance cikin bakin ciki da damuwa.
Ya ce: "Na san ba laifin Adam ba ne. Na san hukuncin Allah ne ya sa aka same shi. Idan da a ce na yi tunanin shi ne mai laifi ai da na bar shi a Syria an kashe shi. Idan da ni mugu ne da na kashe shi, amma ban yi haka ba. Sai na bar shi ya rayu har ma na biya kudi ma fanso shi tare da matata.
"Amma a lokacin da IS suka zo suka kashe ma dukkan dangi suka dauke matarka, har ma ta haihu da su, ba za mu amince da haka ba, ko da kuwa wane irin addini suke bi."
Ra'ayoyin yaranta sun sha bamban kan yadda suke kallon barin su da mahaifiyarsu ta yi.
Babban danta Haitham yana taya mahaifinsa kishi, inda ya ce ba zai iya karbar dan IS a matsayin dan uwa ba.
"Mahaifiyarmu ta watsar da mu saboda wancan dan nata," in ji shi.
Ya kara da cewa kaninsa Azad na yawan tambayar inda ta tafi amma har ya gaji ya daina.
"Na gaya masa cewa mahaifiyarmu ba za ta dawo ba don haka ya daina sa rai. Daga lokacin sai ya daina neman ta."
Amma ita macen Hawa, wacce ta dinga taya uwar rainon Adam lokacin suna Raqqa - abin ya dame ta sosai.
"Idan mamanmu tana gida komai na tafiya da kyau. Ina ma a ce za ta dawo, amma kuma ban ga laifinta ba don ta yi kewar Adam."

Wasu matan da abin ya shafa
Ba Jovan ce kadai uwar da ta samu kanta a irin wannan tashin hankali ba.
BBC ta zanta da mata 20 'yan kabilar Yazidi da suka haifi yara da mayakan IS - Amma duk cikinsu babu wacce ta samu damar kawo yaran cikin zuri'arta.
An tursasawa mafi yawansu barin yaran a arewacin Syria kafin su koma Iraki.
Daya daga cikinsu ita ce Laila, wacce take da shekara 16 a lokacin da IS suka dauke ta zuwa Syria.
Ta haifi yara biyu da mayakin IS din da ya sace ta, amma wani mayakin Kurdawa ya ce mata 'ya'yan nata "dangin shaidan ne."
"Ban san me zan yi ba. Na so komawa gida amma ba a ba ni zabi ba."
Ta ce burinta shi ne ta koma jami'a ta kuma samu aikin da zai dinga kawo mata kudin da za ta nemo 'ya'yanta.
"Ina so na gan su ko da sau daya ne kafin na mutu. Ba ni da wani buri bayan wannan."
Ta yi fushi matuka kan yadda majalisar koli ta kabilar Yazidi ta ki sassauta dokokinta da suka haramta karbar 'ya'yan da aka haifa da mayakan IS.
"Wani lokacin sai na dinga ganin tamkar mazajen kabilar Yazidi ba su da imani. Su ba mata ba ne, ba uwaye ba ne, don haka ba za su taba fahimtar yadda muke ji ba."
Mace daya ce kawai daga cikin matan da BBC ta yi magana da su aka bar ta ta rike dan da ta haifa da mayakan IS.
An sayar da Rojin da 'yarta mai shekara hudu ga mayakan IS daban-daban har su bakwai.
Ta dawo gida Iraki ne dauke da cikin wata biyu.
Likitanta ya ba ta shawarar tun da cikin karami ne to ta yi kokarin shawo kan mijinta ya yi kamar dan nasa ne.
Ya yarda, bayan da ta nuna masa cewa idan suka samu da za su fi saurin samun mafaka a wata kasar idan har suka nema.
Amma duk da haka fa tsoro da fargaba ba su sake ta ba.
"Idan har dangina ko kuma wasu 'yan kabilar Yazidi suka gane gaskiyar batu kan dana to fa za su raba ni da shi kuma su tursasa ni na bar gidana su kuma raba ni da daya 'yar tawa.
'Kullum sai na yi tunaninsa'
Jovan na ta karbar shawarwari da kwantar da hankali cikin wata 18 da suka gabata, amma har yanzu tana cike da alhini.
A wani dan littafinta ta zana yadda ranakun da suka shafe a Raqqa suka kasance - inda zanen ke nuna jirgin yaki yana wucewa ta saman gidan da suke, ita kuma da yaranta hudu suna ta sabgogi.
"A wasu lokutan na kan yi tunanin rayuwa ta fi dadi a karkashin IS. An yi mana kawanya, kuma rayuwa ta tsananta, amma dai ina tare da duka 'ya'yana.
"Ban ji wani rauni ba a tsawon shekara hudun nan, amma da na dawo Iraki an ji min raunin da ba zai warke ba.
"An ji min rauni saboda yadda dangina da al'ummata da dokoki suka raba ni da 'ya'yana."
Ta yi fushi mai tsanani da mijinta ta kuma jin takaicin abin da al'ummarta ta yi mata, don haka ne ma ta yanke shawarar ci gaba da zama cikin musulunci.
"Ba na son ci gaba da zama a cikin al'ummar Yazidi... gaskiyar magana ita ce saboda addini ne duk na samu kaina a wannan halin aka raba ni da iyalina."
Amma tana tsoron cewa har abada an raba ta da sauran manyan 'ya'yanta ukun kenan.
"Babban tsoro na shi ne dukkan yarana za su manta da ni su kuma ki yafe min saboda barin su da na yi. Amma ina yawan rarrashin kaina cewa ba za su taba manta mahaifiyarsu ba."
A cewar Sakineh ta gidan marayu, Jovan za ta iya karbo Adam daga wajen wadanda suka dauki rikonsa idan dai har ta iya tabbatar da hakan ta hanyar gwajin kwayoyin halitta cewa ita ce mahaifiyarsa.
Haka kuma duk da cewa Jovan 'yar kabilar Yazidi ce, kuma dan an yi masa rijista a matsayin Musulmi saboda mahaifinsa, hakan na iya kawo cikas a lamarin.
A halin da ake ciki a yanzu dai Jovan ta ce ta amince cewa Adam na cikin yanayi mai kyau a duk inda yake.
"Kullum sai na yi tunaninsa. Amma ina tunanin a yanzu gara dana ya zauna da wasu iyalan. Hakan ya fi masa alkhairi."
Yanzu dukkan burinta da mafarkinta ya ta'allaka ne a kan ta sake haduwa da dukkan 'ya'yanta hudun.
"Ina fatan wata rana , idan har Allah ya ji kaina za mu sake ganin juna."
An sauya wasu sunayen don kare wadanda aka yi hirar da su.












