Sarkin Dubai zai gurfanar da matarsa gaban kotu

Gimbiya Haya ta tsere wa mijin nata daga Dubai inda yanzu take zaune a Landan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gimbiya Haya ta tsere wa mijin nata daga Dubai inda yanzu take zaune a Landan
An wallafa

A ranar Talatar nan ne daya daga cikin manyan hamshakan shugabanni masu arziki da matsayi a Gabas ta Tsakiya zai kai karar matarsa da suka samu sabani, gaban wata kotu a Landan.

A shari'ar wadda ta dauki hankalin duniya, Sheikh Mohammed Al-Maktoum, mai shekara 69, da ke mulkin Dubai zai kai karar Gimbiya Haya a kan batun kula da 'ya'yansu.

Gimbiya Haya mai shekara 45, wadda 'yar uwar sarkin Jordan ce, ta tsere daga Dubai zuwa Landan a farkon shekarar nan, kuma abokananta sun ce tana cikin fargaba game da rayuwarta.

Shugabannin kasashen Larabawa na yankin Fasha galibi suna daga cikin mutanen da a duniya suke tafiyar da harkokinsu na rayuwa cikin sirri, to amma wannan shari'ar tuni ta dauki hankalin duniya.

Sarkin na Dubai wanda yana daya daga cikin hamshakan masu hannu a gasar sukuwar dawakai ta duniya, yana da dukiyar da ta kai ta sama da fam biliyan uku.

An ruwaito cewa ya rubuta wata waka ta bacin rai wadda a ciki yake zargin wata mata da bai ambaci sunanta ba da cin amana.

Gimbiya Haya tare da Yarima Charles da matarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ganin Gimbiya Haya wadda ta yi makaranta a Dorset da Oxford tana son zama ne a Birtaniya

Da farko Gimbiya Haya ta gudu Jamus a shekarar nan inda ta nemi mafaka. Daga baya kuma ta tafi Landan, inda yanzu aka ce tana zaune a wani gida da kudinsa ya kai dala miliyan 107 aKensington Palace Gardens, a tsakiyar Landan.

Wata shakikiyar Gimbiyar ta bayyana cewa, a kwanan nan ta gano wani zargi da ake yi na tilasta mayar da daya daga cikin 'ya'yan Sarkin mata, zuwa Dubai, a shekarar da ta wuce.

Yarinyar ta uku daga cikin 'ya'yan gidan sarautar Sheikh Mohammed, ta tsere a 2001, kuma ana zargin an sace ta a Cambridge aka mayar da ita Dubai.

Rahotanni sun ce Sheikh Mohammed yana da 'ya'ya 23 da ya haifa da mata daban-daban.

Ana ganin Jordan ba za ta ji dadin wannan shari'a ba, saboda Gimbiya Haya kanwar Sarki Abdullah na Jordan ce, kuma akwai 'yan Jordan kusan dubu 250 da ke aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa, suke tura kudade gida, wanda a kan hakan Jordan ba za ta so ta samu sabani da Dubai ba.