Kalli hotunan yadda Amurkawa ke maganin tsananin zafi

Yara na wasan ruwa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yara na wasan wanka a wurin shakatawa na Domino Park, a New York
An wallafa

A yanzu Amurka na fuskantar yanayi mai tsananin zafi, inda ya kai lamba 38 a ma'aunin Selshiyas.

Lamarin ya fi tsanani a jihohin da ke yankin gabar gabas (East Coast) ta tekun kasar, inda jama'a a New York da Philadelphia da kuma Washington suke fama da dan-karen zafi.

Daman kusan wadannan jihohi sun fi Phoenix da Arizona da kuma Miami a Florida zafi.

An bukaci mutanen yankunan da abin ya shafa da su tabbatar suna shan wadataccen ruwa, sannan kada su fita waje idan ba ya zama dole ba, kuma su rika kula da mutane masu rauni, wadanda suka hada da marassa lafiya, da yara da kuma tsofaffi.

A man looks outside his window in New York

Asalin hoton, Reuters

Mutane na kokarin sanyaya jikinsu ta duk wata hanya da za su iya, inda ake ganin mutane sun cika a tafkunan wanka na gwamnati da duk inda ake da ruwa da ke zuba.

Tafkin wanka na Astoria Pool da ke Queens, a New York City, ya cika da jama'a a ranar Asabar.

People enjoy the Astoria Pool on a hot afternoon in the borough of Queens, New York City, on July 20, 2019

Asalin hoton, AFP

Wannan yaron shi kuwa ya je wurin famfon da ke watsa ruwa ne na jika shukoki, yana jika jikinsa saboda maganin zafin, a kusa da Astoria Park.

A boy cools down in a spring in the Astoria Park in the borough of Queens on July 20, 2019

Asalin hoton, AFP

Magajin garin birnin New York Bill de Blasio ya ayyana cewa birnin na cikin yanayi na tsananin zafi, kuma a karon farko cikin shekara 18 an soke gasar tseren keke da linkaya da kuma gudu ta birnin wadda a da za a fara ranar Lahadi.

Kusan mutane 4,000 ne aka sa ran za su shiga gasar, inda yawancinsu kan je daga wurare masu nisa domin halarta. Masu shirya gasar sun ce za a mayar wa da masu shiga kallon gasar cikakken kudin tikitinsu, wanda ya kai dala 399.

An samar da wuraren wanka ko jika jiki sama da 500 ga mazauna birnin New York City.

A Boston da ke Massachusetts, mutane manya da yara na ta tururuwa zuwa wuraren da ake da inda ruwa ke zuba domin sanyaya jikinsa.

Kids and adults cool off in a fountain on the Rose Kennedy Greenway on the first day of a forecasted summer heatwave in Boston, Massachusetts

Asalin hoton, Reuters

Wata yarinya na wasa da ruwa a lambun Rose Kennedy Greenway a ranar farko da aka yi hasashen tsananin zafin a Boston, Massachusetts

Asalin hoton, Reuters

Wani dan yawon bude idanu ne nan ya kare kansa daga zafin rana da littafin jagora ko sanin gari na fadar White House.

Dan yawon bude idano ya kare kansa daga zafin rana

Asalin hoton, Getty Images

Ba mutane ne kadai suke cin moriyar ruwan sanyin ba. Su ma wadannan tsuntsayen biyu ba a bar su a baya ba, kamar yadda ake gani an dauki hotonsu suna wanka a lambun Rose Kennedy Greenway a Boston.

Tsuntsaye na wanka a lambun Rose Kennedy Greenway

Asalin hoton, Reuters

A Philadelphia, an ga wani kare yana sanyaya jikinsa a wani wurin abin kashe gobara.

Wani kare na wanka a wani wurin abin kashe gobara

Asalin hoton, Getty Images