Bincike: Watan Yunin 2019 ne mafi tsananin zafi a duniya

An wallafa

Duniya ta fuskanci yanayin zafi mafi tsanani a watan Yunin 2019 inda alkalumman bincike suka ce ma'aunin ya kai 61.6F.

Hukumar kula da yanayi da teku a Amurka ta ce matsakaicin yanayin ya fi tsanani fiye da na karni na 20 da aka taba gani.

Hukumar ta ce zafin ya fi tsanani a Nahiyar Turai da Rasha da Canada da kuma kudancin Amurka.

Rahoton na zuwa ne a yayin da Amurka ke shirin tunkarar yanayin zafi mai matukar hatsari.

An yi gargadin cewa miliyoyin mutane a duniya ne za su yi fama da zafin da ke tafe a kwanaki masu zuwa a Amurka.

Magajin birnin New York Bill de Blasio ya wallafa a Twitter cewa "juma'a ba za ta yi dadi ba, kamar yadda zafin zai fi muni a ranar Asabar"

Tara daga cikin goma na watannin Yuni mafi tsananin zafi daga 1880 zuwa 2019 sun faru a tsakanin shekaru tara da suka gabata.

Yunin 2018 ya doke na 2016 a matsayin wata mafi tsananin zafi da aka taba fuskanta a duniya.

Masana kimiya sun yi gargadin cewa za a ci gaba da fuskantar yanayi na tsananin zafi saboda canjin yanayi.