Kalli hotunan yadda zafi ya addabi nahiyar Turai

An wallafa

Mutane da dama a fadin nahiyar Turai na kokarin kaucewa tsananin zafi da ake fama da shi a lokacin da yanayi ke kara hauhawa.

Yanayin wanda masana suka ce ka iya yin kisa - ya tsananta ne saboda iska mai zafi da ke fitowa daga yankin Sahara - kuma tuni ya sa aka soke jarabawar 'yan makaranta a Faransa.

Sai dai masanan na hasashen yanayin zafin a kasashen Faransa da Jamus da Belgium zai iya kai wa matsayin da ba a taba gani ba a 'yan kwanaki masu zuwa.

Duka hotunan na da hakkin mallaka