Kun san riga-kafin kisa daga tsananin zafin rana?

    • Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Matsanancin zafin da ake yi a yammacin Turai ya sa mutane suna tunawa da irin wanda aka taba yi a shekarar 2003, inda dubban mutane suka mutu a nahiyar.

Ba a faye yin matsanancin zafi ba a Turai, sannan kuma ba a saba yin zafin a farkon bazara ba kamar watan Yuni.

An tanadi ayyukan agaji na ko-ta kwana saboda shawo kan duk matsalar da ka iya tasowa.

Ba a Turai kawai ake wannan zafin ba - fiye da mutum 100 ne suka mutu a Bihar na arewacin Indiya inda yanayin zafin ya wuce 50C a ma'aunin salshiyas.

To ta ya ya zafi ke kisa ne, kuma me za mu yi don kare kanmu daga yanayin zafi mai tsawo?

Wa abin ya fi shafa?

Yawan mutanen da matsanancin zafi ke shafa ya karu a karni na 21.

A tsakanin shekarun 2000 zuwa 2016, yawan mutanen da zafi ke shafa ya karu da kusan miliyan 125, a cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO.

A wannan lokacin an ga yanayin zafi mai tsanani da suka hada da a 2003 inda mutum 70,000 suka mutu a Turai sakamakon tsananin zafi. A shekarar 2010 ma an samu mace-mace guda 56,000 sakamakon matsanancin zafin da aka yi na kwana 44 a Tarayyar Rasha, kamar yadda WHO ya tabbatar.

WHO ta ce "Tsofaffi da yara da masu juna biyu da masu aikin karfi da masu wasanni da kuma marasa galihu,"su ne abin ya shafa.

Tsofaffi da masu juna biyu da yara na cutuwa ne saboda kariyar jikinsu na yin kasa.

Su kuwa masu aikin karfi a waje kamar manoma da marasa muhalli abin ya fi shafar su ne saboda suna shiga cikin rana.

Yawan motsa jiki kuma na sa jikin bushewa wanda hakan ke sa wa masu wasanni ke shan wahala a lokacin zafin.

Alakar zafi da jiki

Da yake yanayin jinin jikinmu mai dumi ne, hakan ya sa jikin ba ya iya jure wa yanayin zafin da ya kai 37 a ma'aunin salshiyas.

A yayin da zafin muhallin da muke zaune ya karu, jiki ba ya iya jurewa zafin.

Dakta Davron Mukhamadiev ya ce: "Idan zafin gari ya dade har ya fi na cikin jikinmu yawa zai zama barazana ga lafiyarmu."

Zuciya tana tunkudo jini a-kai-a-kai zuwa sauran jiki, inda daga nan ne zafin yake fita daga jiki zuwa iska. Wannan dalili ne ya sa fatar wasu take zama launin ja a yankuna masu zafi.

Alamun cutar da zafi ke haifarwa

  • Ciwon kai, jiri, rashin annashuwa
  • Rashin natsuwa da dimaucewa
  • Zafi da kuma bushewar fatar jiki
  • Zafin jiki sama da 40C
  • Bugun zuciya cikin sauri

(Majiya - St John Ambulance. UK)

Gumi

Sannan kuma muna yawan yin gumi. Yin gumi yana taimakawa wajen sanyaya jiki, sai dai ba zai yi aiki yadda ya kamata ba idan zafin gari ya zama daidai ko ya fi na fatar jikinmu yawa.

'Idan zafi ya kai sama da 37C yana da hadari sosai. Ko da a lokacin da zafin yake a 30C ya kamata mu fara daukar matakin kare kanmu.

"Daukewar iska ma yana da hadari sosai domin kuwa yana zama abu mai wuya ga mutane su yi gumi kuma su dan sarara a irin wannan yanayi," in ji Dakta Mukhamadiev.

Mutane kan fuskanci jiri da ciwon kai har da suma idan zafin ya kama su.

Illar zafi ga jiki

Da farko-farko ya kan haddasa kumburi da kuma kurajen zafi.

"Yayin da muke ayyuka ba-ji-ba-gani, kofofin jini kan kara girma kuma ruwan jiki ka iya bulla zuwa jikin bangon kafafu. Hakan yana haddasa kumburin kafa ko idan-sahu da wasu ke fuskanta," in ji hulkumar lafiya ta Birtaniya.

Fitar ruwan jiki ta hanyar gumi da kuma saukar jini kan haifar da babbar matsala ga jiki.

Bugun zuciya

Idan mutum ya kamu da cutar tsananin zafi na tsawon lokaci to zai iya haifar masa da bugun zuciya.

"Yin gumi zai janyo kafewar ruwan jiki, wanda kuma yake rage yawan jini a jiki. Kazalika shi ke sa zuciya ta kasa tunkudo jini da karfi yadda ya kamata," kamar yadda Ony Stubbs, shugaban cibiyar ya fada Australian Heart Foundation.

Ya kara da cewa "tsananin zafi ka iya haddasa mutuwa ga mutanen da ke da ciwon zuciya wadanda kuma ke cikin hadarin kamuwa da bugun zuciya".

Cutar tsananin zafi

Cutar tsananin zafi na faruwa ne yayin da bangaren hypothalamus a cikin kwakwalwa, wanda yake da alhakin kula da ayyukan sauran sassan jiki kamar yin gumi.

Hukumar kula da ayyukan kiwon lafiya a Birtaniya (NHS) ta ce: "Cutar tsananin zafi kan faru yayin da zafin jiki ya wuce 40C, wanda hakan ke hana kwayoyin halitta da sauran sassan jiki yin aiki yadda ya kamata."

Idan hypothalamus ya gaza yin aiki, jikin dan adam kan gaza yin aiki yadda ya kamata, saboda haka sai ya kasa bayar da kulawa ga yanayin gumin jiki.

"Wadanda abin ya shafa za su iya fuskantar matsalar numfashi da ciwon kai da dimaucewa. Idan dai har ba a samu kulawar gaggawa ba, to gabobin jiki ka iya daina aiki wanda kuma zai iya kai wa ga mutuwa," in ji NHS.

Mutuwa

Dubban mutane ne ke mutuwa a kowacce shekara a kasar Indonesia da Mexico saboda cutuka masu alaka da yanayin zafi.

"Mutane ka iya mutuwa cikin 'yan sa'o'i idan zafin gari ya wuce 38C zuwa 42C tare da daukewar iska, inda a lokacin nan jiki ba zai iya jurewa ba" in ji Dakta Mukhamadiev.

Hutu a-kai-a-kai da kuma rage yawan lokutan da muke batawa wajen ayyukan yau da kullum ka iya taimaka wa jiki farfadowa cikin sauri.

Yadda za ka guje wa tsananin zafi

  • Guje wa zafi: kada ka shiga rana, sannan kada ka fita waje tsakanin karfe 11 zuwa 3 na rana (lokaci mafi tsananin zafi kenan)
  • Yi amfani da abu mai shara-shara kuma maras nauyi ka rufe tagogi
  • Ka yi wanka lokaci-lokaci sannan ka rika watsa wa kanka ruwa
  • Ka rika shan ruwa a-kai-a-kai sannan ka guji shan giya - ruwa da madara da shayi suna taimaka wa jiki
  • Ka saka kaya marasa nauyi kuma masu shara-shara
  • Ka saka bakin gilashi da malafa idan za ka fita waje
  • Ka rika tuntubar 'yan uwa da abokan arziki da makota wadanda ba lallai ne suna cikin koshin lafiya ba

(Majiya NHS UK)

Tsira tsananin zafi

Ana shirya wa tsananin zafi a birane da dama, inda hukumomi suka tsara matakan da za a dauka domin tsira daga abin da ka iya faruwa.

Kazalika, da alama jikin dan Adam ma zai iya yin nasa kokari.

Wani rukunin masu bincike a jami'ar Harvard ya gano cewa, cutuka masu alaka da zafin yanayi sun ragu daga shekarar 1987 zuwa 2005 a kasashe 105.

"Al'umma na tsira daga tsananin zafi a tsawon lokaci," binciken ya fada. Sai dai har yanzu akwai sauran aiki.

Binciken ya yi gargadin: "karuwar maki biyar na yanayin zafi a kan yadda aka saba wanda ka iya janyo mutuwar mutum 1,907 a kowace bazara a biranen duniya."

Riga-kafi

Mutum zai iya kare kansa daga hadarin kamuwa da cutar tsananin zafi da makamantanta.

"A takaice dai, ba a so mutum ya kasance a waje na sama da sa'a biyu ko uku a wurare masu tsananin zafi. Yana da matukar amfani mutum ya rika shiga inuwa musamman tsakanin karfe 10 na safe zuwa 5 na yamma," in ji Dakta Mukhamadiev.

"Ka kula da kanka da 'yan uwa da abokan arziki. Kiran waya daya da za ka yi zai iya ceton ran wani."