Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan sabbin wuraren ban mamaki na duniya
Duk shekara akan zabo wasu fitattun wurare da Allah Ya halitta ko kuma masu alaka da al'adun bil-Adama a fadin duniya saboda darajarsu ga al'ummar duniya.
Hukumar raya Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta sha gudanar da taruka a birnin Baku na Azerbaijan domin tantance wuraren da suka dace a zaba.
Ga wasu karin wuraren da suka shiga jerin kawo yanzu.
Gandun Namun Dajin Vatnajökull na Iceland
Wannan yankin da ake yawan samun aman duwatsu ya mamaye kusan kashi 14 cikin 100 na fadin Iceland.
Gandun na cike da duwatsu masu kama da gilashi da kuma wasu duwatsun masu kayatarwa, ciki har da filayen da aman wuta ya mamaye da dabbobi na musamman.
Filaye da Tekunan yankin Australiya masu amfani da harshen Faransanci
An bayyana wurin a matsayin wani wuri mai ni'ima a tekun kudancin duniya, kwamitin raya al'adu na Majalisar Dinkin Duniya ya zabi wurin mai tsibirai jefi-jefi a matsayin daya daga cikin wurare masu daraja.
Ana samun tsuntsaye da kuma dabbobin ruwa na musamman a duniya.
Birnin Jaipur na Indiya
An yi wa birnin Jaipur na Indiya, da ke arewa maso yammacin kasar lakani da "birni mai kalar hoda".
Yawancin gine-ginen da ke birnin an yi su ne tun a lokacin da aka gano birnin a shekarar 1727 kuma an kawata gaban gine-ginen.
Hubbare mai tarin kasa na Japan ta zamanin da.
Wadannan hubbaren guda 49 an gina su ne a karni na uku da na shida a birnin Osaka na Japan.
Tarin kasar na da nau'i daban-daban cikinsu har da guda daya mai kirar inda ake soka makulli wanda aka sa wa sunan Sarki Nintoku - shi ne hubbare mafi girma a Japan.
Babylon a Iraki
Bayan shekaru da dama da birnin ya yi ta nema ya kasance a cikin jerin biranen Unesco, sai yanzu birnin Mesopotamian na zamanin da na Babylon ya samu damar shiga jerin.
Wurin ya dade yana ta lalacewa saboda rikicin da kasar Iraqi ke fama da shi, amma a 'yan kwanakin nan an yi wa wurin kwaskwarima.
Bagan a Myanmar
Dubban wuraren bauta na mabiya adinnin Budha a filin mai kayatarwa, shi ya sa masu yawon bude ido ke tururuwar zuwa wannan tsohon birnin.
Filin Tuluna a Laos
Wuraren da ke dauke da masu manyan tuluna a Xiengkhouang, birnin Laos, su ma sun samu shiga wannan jerin.
Masu hako kayan tarihi sun yarda cewa an sassaka dubban duwatsun ne a zamanin da ake yawan amfani da dutse a matsayin kabari.
All images copyright.