An cimma matsaya a rikicin Sudan

Asalin hoton, AFP
Majalisar sojoji mai mulki a Sudan da shugabannin adawa sun sa hannu a kan wata yarjejeniyar raba iko bayan kashe dare suna tattaunawa.
An sa hannu kan yarjejeniyar ne a Khartoum, babban birnin kasar a gaban masu shiga tsakani na Kungiyar Kasashen Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na AFP sun ruwaito Mohamed Mohamed Hamdan "Hemeti" Dagolo na cewa wannan wani al'amari ne na tarihi a kasar.
Ya ce "ina farin ciki yi wa 'yan Sudan albishir kan wannan babban al'amari na sa hannu kan yarjejeniyar siyasa."
Sojoji dai sun kwace mulkin ne bayan sauke Omar al-Bashir a watan Afrilu.
Ana sa rai wannan yarjejeniya za ta kawo karshen tashin hankalin da kasar ta fuskanta a baya-bayan nan, kuma za a kafa gwamnati hadin gwiwa ta shekara uku inda kuma daga karshe za a gudanar da zabe.

Asalin hoton, AFP
Sai dai wata mai magana da yawun daya daga cikin manyan kungiyoyin fararen hula ta nuna halin ko in kula kan yarjejeniyar.
"Ba wani abin a zo a gani bane," in ji Dakta Sara Abdelgalil, kakakin kungiyar kwadago ta Sudan Professionals Association.
"Wannan shi ne matakin farko na raba iko, amma babu bayanai sosai a kansa. Mataki na biyu na tattaunawa shi ne ayyanawa a hukumance. Wannan matakin ne na fargaba da fata. Babu wani abin murna a cikinsa."











