Yadda gobarar tankar fetur ta hallaka mutane a Benue

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin agaji na jihar Benue sun ce ana ci gaba da ayyukan ceto a wajen da wata gobarar tankar man fetur ta faru, ko za a samu karin gawarwakin wadanda suka mutu a wajen.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC reshen jihar Benue ta ce a kalla mutum 35 ne suka mutu yayin da fiye da 50 suka jikkata a lokacin da wata tankar dakon mai ta fadi a titi a yankin jihar da ke tsakiyar Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa motar ta fadi ne a kusa da wasu shaguna yayin da take wucewa ta kauyen Ahumbe na jihar Benue a ranar Litinin.
Mazauna kauyen sun yi ta rububin zuwa kwasar man fetur din, amma sai motar ta yi bindiga - al'amarin da ya jawo tashin gobara a illahirin yankin.
Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Benue Aliyu Baba, ya shaida wa AFP cewa: "Mun kwashe a kalla gawarwaki 10 daga wajen da abin ya faru, yayin da wasu 50 kuma suka jikkata."
"Ganin yadda girman gobarar yake, ina fargabar ba mamaki a iya kara gano wasu gawarwakin yayin da ake ci gaba da aikin ceto a ranar Talata."
Wani mai magana da yawun karamar hukumar wajen ya ce yawan wadanda suka mutu zai kai 64, amma 'yan sanda sun ki tabbatar da yawan wadanda suka mutun.
Wani ganau Otukpa ya ce akwai wata motar bas mai daukar mutum 14 da gobarar ta rutsa da ita kuma mutum daya ne ya tsira a cikinta.
Hatsarin tankokin dakon man fetur ya zama ruwan dare a Najeriya, kasar da duk da cewa tana da arzikin mai da iskar gas, amma mafi yawan al'ummarta na zaune cikin talauci.
Gobarar na yawan tashi ne a yayin da mutane suke rububin kwasar man fetur din da ya zube, sannan motocin kan fadi ne sakamakon rashin kyawun hanya.
A watan Janairun ma mutum takwas ne suka mutu a garin Odukpani a kudu maso gabashin jihar Cross River a wani hatsarin irin wannan.











