Tankar mai ta kama da wuta a wani banki a Legas

Bayanan bidiyo, Tuni dai 'yan kwana-kwana suka isa wajen kuma suka samu nasarar kashe wutar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Wata tankar mai ta kama da wuta yayin da ta ke sauke man dizel a hedikwatar Bankin Ecobank da ke Victoria Island a Legas.

Al'amarin ya faru ne da misalin karfe takwas na safiyar Talata, a lokacin da tankar ke sauke man dizel a bankin.

Lagos tanker fire happun for Eco bank

Tuni dai 'yan kwana-kwana suka isa wajen kuma suka samu nasarar kashe wutar.

Zuwa yanzu dai babu asarar rayuka, amma babu tabbas ko akwai wadanda ba su ji ciwo ba.

Wannan ne karo na biyu a cikin wata guda da tankar dakon man fetur ta kama da wuta a Legas, inda na farkon ya faru a kusa da Gadar Otedola kan babban titin Lagos zuwa Ibadan a watan Yuni.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X