Gobara ta hallaka mutum 55 a Nijar

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Akalla mutum 55 ne suka mutu sakamakon gobarar tankar dakon mai a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi.
Hukumomin kasar sun ce akwai kuma wasu 30 da suka samu munanan raunuka.
Babban darakta a hukumar kare hakkin farar hula, Kanar Boubacar Bako ya ce lamarin ya faru ne a cikin dare kusan da filin jirgin sama.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne bayan mutane sun yi dafifi, inda tankar ta fadi a kokarin kwasar mai abin da ya haddasa ta yi bindiga.
Firai Ministan kasar da wasu ministocinsa sun ziyarci inda aka samu iftila'in, kafin daga bisani suka wuce asibiti domin duba halin da wadanda suka ji rauni suke ciki.
Karanta wasu karin labarai







