Za a yi gagarumar zanga-zanga a Sudan

An wallafa

Hukumomin soji da ke mulki a Sudan sun ce za su dora alhaki a kan 'yan hamayya, muddin aka samu rasa rai ko asarar dukiya a wata zanga-zanga da 'yan hamayyar suka shirya yi ranar Lahadi.

Daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke fafutukar ganin sai sojin sun mika mulki ga farar hula, ta zargi sojin da tarwatsa wani taron manema labarai da ta shirya ranar Asabar, a kan shirye-shiryenta na zanga-zangar ta Lahadi.

Gangamin zai kasancewa na farko tun bayan da jami'an tsaro suka yi amfani da karfin tsiya wajen tarwatsa wata zanga-zangar a ranar uku ga watan nan na Yuni, a Kahartoum.

Matakin na jami'an tsaro ya yi sanadiyyar mutuwar gwamman farar hula da jikkata daruruwa a babban birnin Sudan din.

Kungiyoyin 'yan hamayyar na Sudan, wadanda suka lashi takobin ganin sai sojojin kasar sun mika mulki ga farar hula, sun bijiro da wannan zanga-zangar ce ta Lahadi, da zummar za ta kasance mafi girma tun bayan ta ranar uku ga watan nan na Yuni.

Sojojin dai sun dora alhakin wannan rikici da ya barke a wancan lokacin a kan wadanda suka kira, wasu da suka yi kutse cikin masu zanga-zangar, duk kuwa da shedu da yawa da suka tabbatar sojojin ne suka far ma jama'ar.

Kafin zanga-zangar ta ranar Lahadi, harwayau sojojin sun yi gargadin cewa za a iya samun wasu masu zagon-kasa da za su garwaya a ciki su tayar da hatsaniya.

Sojojin sun yi wadannan kalamai ne na zargi duk kuwa da cewa sun yi alkawarin samar da tsaro ga masu zanga-zangar.

Kungiyoyin farar hula da ke shirya zanga-zangar suna zargin sojojin da ci gaba da kokarin murkushe su.

Daya daga cikinsu, kungiyar kwararru, ta Sudan Professionals Association, ta ce jami'an tsaro sun yi wa hedikwatarta dirar-mikiya ranar Asabar, jajiberin zanga-zangar, inda suka hana taron manema labarai da aka shirya kan gangamin.

Hukumomin sojin na Sudan sun ce sun amince da shawarar da kungiyar kasashen Afirka, AU, ta bayar, ta farfado da tattaunawa da hadakar 'yan hamayya.

Sai dai ana ganin wannan labari ba lalle ba ne ya sa masu zanga-zangar su fasa aniyarsu ta fantsama kan tituna, a fafutukar tasu ta neman sai soji sun mika mulki ga farar hula.