Sojojin Sudan sun ki amincewa da jagorancin farar hula

An wallafa

Wani babban jami'i a gwamnatin mulkin soja ta Sudan ya shaida wa BBC ba za su bar fararen hula su mamaye majalisar kolin shugabancin kasar ba yayain bada mulki.

Laftanar Janar Salah Abdelkhalek ya ce, dole ne fararen hula su yarda da raba daidai a jagorancin kasar.

Masu zanga-zangar na ci gaba da zaman dirshen a wajen shalkwatar rundunar sojojin tare da bukatar sojoji su bar mulki.

An hambare Shugaba Omar Al-Bashir daga mulkin Sudan a ranar 11 ga watan Afirilun da ya gabata bayan share shekaru 30 kan kujerar shugabancin kasar.

Sojoji ne suka maye gurbin Al-Bashir tare da yin alkawarin za su bada mulki ga gwamnatin farar hula cikin shekaru biyu, wanda masu zanga-zanga suka nuna kin amincewa da hakan.

Shugabannin masu zanga-zangar sun zargi sojojin da kin tattaunawa da su tare da kokarin dorawa akan muraden Mista Bashir.

Su kuma shugabannin sojojin na cewa akwai bukatar su rike kasar na dan lokaci domin tabbatar da doka da oda da kuma cikakken tsaro a kasar.

Me janar din ke cewa?

Laftanar Janar Salah Abdelkhalek ya shaida wa BBC cewa, ana cikin wani matsanancin hali ne, kamata yayi a yi raba daidai tsakanin soji da fararen hula a majalisar kolin.

Har yanzu dai babu takamaiman bayanin yadda majalisar kolin zata rika aiki, amma da yiwuwar ta zama sama da gwamnati, wacce za ta zama cike da kwarraru da fararen hula kamar yadda wakilin BBC ya shaida.

Laftanar Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ne ke jagorantar gwamnatin rikon kwaryar sojojin mai mambobi bakwai, kuma ya shaida wa BBC a watan da ya gabata cewa a shirye yake ya mika mulki ga gwamnatin farar hula amma idan aka cimma yarjejeniya da shugabanninsu.

A ranar Alhamis ne shugabannin 'yan hamayya suka aika da daftarin kundin tsarin mulkin kasar zuwa kwamitin shugabannin sojojin inda suka ce har yanzu suna jiran martaninsu.

Daftarin ya bayyana ayyukan sabuwar gwamnatin rikon kwaryar karara, amma bai bayyana su wane ne za su kasance cikin majalisarta ba.

Tun da farko kungiyar kasashen Afrika ta AU ta baiwa shugabannin sojoji kwanaki 15 domin su mika mulki ga farar hula, yanzu kuma sun basu kwana 60 kacal domin mika mulkin ko kuma su dakatar da sudan daga kungiyar.

Ina Bashir?

Tsohon Shugaban Omar Al-bashir mai shekaru 75, an mika shi gidan yarin Kobar da ke Khartoum kwanaki kadan bayan hambarar da gwamnatinsa.

Wani mai gabatar da kara ya bada umarnin a tuhumi tsohon shugaban kasar kan halasta kudaden haram da kuma daukar nauyin 'yan tada'adda.

Hukumomin kasar sun gano wata jaka cike da makudan kudade sama da dalar Amurka dubu 351, sai kuma biliyan daya na fan din Sudan a wani samame da suka kai gidan al-Bashir din a watan da ya gabata.