An kashe masu zanga-zanga a Sudan

Rikicin Sudan

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Bayanai daga Sudan na cewa an kashe masu zanga-zanga uku da wani jami'in tsaro daya yayin wani artabu a babban birnin Khartoum.

Majalisar soji da ke jagorantar kasar tun bayan hambaras da shugaba Omar Al-Bashir a watan jiya ta ce an jikkata masu zanga-zanga da dama.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ci gaba a tattaunawa tsakanin sojoji da wata gamayyar 'yan adawa wajen kafa hukumar da za ta jagoranci kasar.

Daya daga cikin masu zanga-zangar a Khartoum, babban birnin kasar ta shaidawa BBC cewa "wasu mutane a kayan sojoji" sun harba masu harsashi.

Lina Hieba ta bayyana lamarin a matsayin wani "gagarumin arangama", inda ta ce an kashe wasu masu zanga-zangar yayin da aka rankaya da wasu asibitoci.

Ta yi watsi da kalaman majalisar soji dake cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun harbi masu zanga-zanga, inda ta ce wani yunkuri ne na karkatar da tattaunawar da ake yi tsakanin shugabannin zanga-zangar da sojoji.

"Ba mu yarda da haka ba kuma ba mu amince da su ba," a cewar Ms Heiba.

A baya dai babban mai shigar da kara na kasar ya ce an tuhumi Mista Bashir da wasu mutane bisa kisan masu zanga-zangar.