Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin tsugune ba ta kare wa Sudan ba?
Tun bayan guguwar neman sauyi da ta kada a yankin gabas ta tsakiya shekaru takwas da suka gabata, yankunan ke fuskantar gagarumin sauyi.
A lokuta da dama ba a fiye kalubalantar gwamnatoci da ke mulki ba.
A wasu wuraren kuma akan kafa sabuwar gwamnati ba tare da ba ta lokaci ba kamar a Masar, amma a Syria tafiyar hawainiya ake gani.
Sai dai rikicin da ake yi da zub da jini a Syria akwai hannu da kuma rawar da kasashen katare ke takawa.
Yanzu dai ana fargaba da zargin cewar akwai hannun kasashen katare a guguwar rikicin da ke neman kassara Sudan.
Sai dai wannan ba yana nufin Sudan na cikin barazanar fadawa wani yanayi ko rarrabuwar kawuna da kazancewar rikici irin na Syriya ba.
Akwai batutuwa da dama da ake gani kusan sun yi kamanceceniya da halin da gabas ta tsakiya ke ciki da kuma Sudan, misali rawar da Saudiyya ke takawa da kawayenta na yankin Gulf da kuma alakarsu yanzu haka da Qatar da kuma Turkiyya.
Rikicin yankin dai ya kai wani mataki, duk da cewa ana gani kin samun bayanai daga Amurka da ke taka muhimmiyar rawa a rikciin gabas ta tsakiya na tattare da sarkakiya a fanin diflomasiyya.
Kusan kuma haka yake a fanin Rasha, wadda ke amfani da damar ta a Syria domin sake ginan kanta a fanin diflomasiyyar yankin gabas ta tsakiya.
'Nuna halin ko in kula'
Kusan ana iya cewa Saudiyya ta yi kane-kane da kwace ragamar harkokin diflomasiyya.
Saudiyyar da Hadaddiyar Daular Larabawa na taimaka wa Sudan da kudadden tallafi, man fetur da abinci da magunguna.
Abu Dhabi ta dauki nauyin tattaunawa tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai kan makomar Sudan a siyasance.
Kuma kawar Saudiyyar wato Masar, ta taka muhimmiyar rawa a kungiyar hadin-kan kasashen Afirka, wato AU.
Yayin da ake ganin Saudiya na marawa janar-janar din kasar baya, Turkiyya da Qatar na da kusanci sosai da masu tsatsauran ra'ayi addini a Sudan.
A baiyane yake cewa wadannan kasashe ba bukatun mutanen da ke zanga-zangar ne a gabansu ba, sannan babu wani kokari da suke na samar da ci gaba a demokradiyyar Sudan.
Ko da kuwa sun ba da hujjar son ganin an tabbatar da daidaito.
Sai dai abin da ke faruwa a yanzu kokari ne na ganin an ingiza magoya baya su kasance barazana ga makomar Khartoum.
Wasu labarai kan rikicin Sudan:
Idan muka yi waiwaye, kafin aukuwar guguwar sauyin kasashen Larabawa, Amurka na ganin Sudan a matsayin kasar da ke daukan nauyin ta'addanci; baya ga takunkuman da Amurkar ta kakabawa kasar sakamakon rawar da take takawa a rikcin Darfur haka nan kuma tana fuskantar hare-hare makamai masu linzami.
Ana ganin Sudan a matsayi wacce ke kawance da masu tsatsauran ra'ayin Islama na Iran.
Saudiyya ta yi kokarin karfafawa Sudan gwiwar kasancewa cikin hadakar mabiya Sunni.
Ba a bisa kuskure dakarun Sudan suka kasance cikin kawance dakarun da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen ba.
Sai dai a 'yan kwanakin nan an samu sauyi a fannin alfarmar da Sudan ke samu.
A watan Maris din shekarar 2018, Qatar da Turkiyya da Sudan sun sanya hannu a yarjejeniyar bunkasa tashar ruwar Suakin a Red Sea da na'urar taimakawa sojin ruwa a Turkiyya.
Tabbatuwar wannan aiki da Qatar kusan shi ne abin da Shugaba Omar al-Bashir ya sanya a gaba lokacin da zanga-zangar neman ya sauka ta fara a watan Janairu.
Rashin manyan masu taka rawa
Mutane sun nuna jajircewa a zanga-zangar da ta karade tittuna Sudan.
Babu alamar da ke nuna ana tunzura wadannan mutane daga waje.
Sai dai boren na kunshe da bayanai.
Manyan kungiyoyin masu karfin fada aji - Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da kungiyar hadin-kan kasashen Afirka da dai sauransu - ba su taka rawar gani ba.
Gwamnatin Donald Trump ba wani muhimmanci take bai wa Sudan ba.
Kusan a kullum tana sake janye huldar diflomasiyya da kasar.
Kusan a koda yaushe ta kan nuna alamomin janyewa daga alamuran kasar da kuma yunkurin rage yawan dakarunta a kasar.
Har yanzu akwai dakarun Amurka a Syria sai dai duk da hakan akwai barazana ta fuskar diflomasiyya da makomar kasar ke fuskanta.
Masu tsokaci na ganin halin ko-in-kula da Amurka ke nuna wa kan lamuran da ya shafi Sudan rashin dabara ne na cimma manufarta a fannin jagoranci harkokin diflomasiyya da zai iya taimakawa makomar Sudan.
Da dama na ganin cewa abu ne mai yiwuwa Mista Trump ya bijirewa bukatun Saudiyya wacce babbar kawar ce a gare su.