Zinedine Zidane ya ce Hazard yana burge shi

salon wasan Eden Hazard

Asalin hoton, Inpho

Bayanan hoto, Zidane ya yaba da salon wasan Eden Hazard
An wallafa

Kocin Real madrid Zinedine Zidane ya ce a kodayaushe yana yaba wa da salon wasan Eden Hazard.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rohotonni ke alakanta dan wasan da komawa Real Madrid.

A baya dai dan wasan mai shekara 28 ya ce zai yi matukar wahala ya sabunta kwantiraginsa a Stamford Bridge, saboda yana mafarkin zuwa Madrid.

Kwantiragin dan wasan dai zai kare a watan yunin 2020, yayin da rahotonni ke cewa Chelsea na son sayar da shi a karshen kaka.

Zidane ya ce: "Dan wasa ne da koyaushe nake yaba masa saboda hazakarsa."

Zidane, mai shekara 46 ya dawo aikin horar da Real bayan da kungiyar ta sallami Santiago Solari a watan Maris, bayan da ya bar kungiyar a watan Mayun 2018 kwanaki biyar bayan lashe kofin Zakarun Turai na Champions League karo na uku a jere a kungiyar.

A yanzu dai Zidane, wanda kungiyarsa ke ta uku a kan teburin Laliga da ratar maki 13 tsakaninta da Barcelona wadda ke ta daya, zai mayar da hankali kan cinikin 'yan wasa idan an bude kasuwar sayayya.