Aladai sun cinye wata mata bayan ta yanke jiki ta fadi

Aladai

Asalin hoton, Science Photo Library

An wallafa

Kafafan yada labarai a Rasha sun ruwaito cewa aladai sun cinye wata mata 'yar kasar bayan ta yanke jiki ta fadi a kusa da inda aka kewaye su.

Rahotanni sun ce matar ta fadi ne a lokacin da ta je wajen aladun tana basu abinci a wani kauye da ke yankin Udmurtia a kasar ta Rasha.

Maigidan matar ne ya gano gawarta bayan da ya koma gida ya tarar matar ba ta nan, sai ya zaga bayan gidan in da aladun suke kuma a nan ne ya yi kicibus da gawarta.

Ya ce ya ga jini na ta kwarara daga jikinta, kuma bai tarar da ita da rai ba.

Matar dai manomiya ce, wadda kuma suke zaune da mijinta a kauyen inda suke kiwon dabbobi da dama ciki har da aladun.

Tuni dai aka soma gudanar da bincike a kan faruwar lamarin.