Shugaba Trump ya ya jinkirta janye dakarun Amurka daga Syria

Asalin hoton, AFP
Shugaban Amurka yanzu ya ce za a janye dakarun kasar sannu a hankali bayan sanarwar da yayi ta bakatatan cewa za a kwashe su a farkon shekarar nan.
A wani sakon Tiwita, ya ce "Sannu a hankali muna dawo da sojojinmu gida domin su kasance tare da iyalansu, kuma muna ci gaba da yakar abin da ya rage na kungiyar IS a daya bangaren".
Wannan ya biyo bayan kalaman da Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican yayi cewa shugaban zai jinkirta janye sojojin daga Syria.
A lokacin da Mista Trump ya sanar da janyewar, ya ce: "Dukkansu za su dawo gida, kuma gaba dayansu za su dawo yanzu".
Wannan matakin ya tayar da hankulan kawayen Amurka da ma jami'an ma'aikatar tsaro kamar sakataren tsaron Amurka Jim Mattis da Brett McGurk, wadanda suka ajiye aiki jim kadan da fitowar sanarwar.

Asalin hoton, AFP
An kiyasta dakarun Amurka 2,000 na aiki a cikin Syria amma yana yiwuwa ma su zarce haka.







