Daruruwan mutane sun mutu sakamakon bala'in tsunami da girgizar kasa

Bayanan bidiyo, Wannan hoton bidiyon na nuna yadda gidaje ke rushewa
An wallafa

An tabbatar da mutuwar mutum 380 bayan da bala'in tsunami tare da girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta afka wa wani babban birnin a kasar Indonesiya a ranar Juma'ar da ta wuce.

Igiyoyin ruwa sun yi tunkoro har zuwa tsayin tsayin mita uku hakan ya sa ruwa ya shafe tsibirin Sulawesi.

Hotunan bidiyon da aka sanya a kafafan sada zumunta sun nuna yadda mutane ke ta kururuwa tare da tserewa a cikin dimuwa.

Dubban gidaje da asibitoci da otal-otal da kuma shaguna ne suka rushe sakamakon girgizar kasar.

Masu aikin ceto na ta kokari wajen ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su, ko da yake suna fuskantar 'yan wasu matsaloli a aikin ceton nasu.

An rufe babbar hanyar da ta bulla zuwa birnin Palu saboda zaftarewar kasa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasa ransu sakamakon girgizar kasar zai iya karuwa, kuma akwai mutum a kalla 540 da suka samu raunuka, yayin da kuma ba a gano wasu mutum 29 ba.

Mutane na duba jakunkunan da aka saka gawawwaki domin neman 'yan uwansu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutane na duba jakunkunan da aka saka gawawwaki domin neman 'yan uwansu

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawar, Sutopo Purwo Nugroho ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, an gano wasu gawawwakin a gefen gabar teku.

Ya kuma ce ko da al'amarin ya fara faruwa sama-sama a ranar Juma'ar, mutane sun ci gaba da harkokinsu a bakin ruwa, amma kuma da lamarin ya munana sai suka fara tserewa.

Wasu mutane dai sun tsira da ransu ne bayan da suka dirgo daga wani gini mai nisan mita shida.

Mutane tsaye a wajen wasu shaguna bayan afkuwar girgizar kasar a birnin Palu

Asalin hoton, Antara Foto/Rolex Malaha via Reuters

Bayanan hoto, Mutane tsaye a wajen wasu shaguna bayan afkuwar girgizar kasar a birnin Palu

A Palu, daruruwan mutane ne suka shirya shiga gasar su wadda aka tsara farawa a ranar Juma'a.

Babban asibitin birnin ya lalace sakamakon girgizar kasar, inda wasu hotuna da aka nuna a kafar talbijin din kasar suka nuna yadda ake kula da marasa lafiya a wajen asibitin.

Tawagar jami'an lafiya na kula marassa lafiya a waje

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Tawagar jami'an lafiya na kula marasa lafiya a waje
Wata mata na kuka saboda iftila'in da ya faru a garinsu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mata na kuka saboda iftila'in da ya faru a garinsu

Biranen Palu da Donggala na dauke da mutane fiye da dubu 600.

Shugaba Joko Widodo ya ce an tura sojoji wuraren da lamarin ya faru domin taimaka wa jami'an agaji a aikin ceton da suke.

Tuni dai aka rufe babban filin jirgin saman Palu tun bayan afkuwar girgizar kasar.

Kazalika an tura wasu jirage soji domin kai kayan agaji ga wuraren da al'amarin ya afku daga Jakarta.

Sojoji na dauke da kayan agaji domin rabawa

Asalin hoton, Antara Foto/Reuters

Bayanan hoto, Sojoji na dauke da kayan agaji domin rabawa
Hukumar agajin gaggawa ta Indonesia ta ce wasu mutane na bi ta kan bishiyyoyi domin tsallake ruwan saman da ke ambaliya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hukumar agajin gaggawa ta Indonesia ta ce wasu mutane na bi ta kan bishiyyoyi domin tsallake ruwan saman da ke ambaliya

Karanta wasu karin labaran

Map showing the epicentre of the earthquake near Sulawesi island in Indonesia
Presentational white space
Babban asibitin Palu wanda ya rushe sakamakon girgizar kasa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Babban asibitin Palu wanda ya rushe sakamakon girgizar kasa