Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ana kashe mutum 57 kullum a Afrika ta Kudu'
Ministan 'yan sanda Afirka ta kudu Bheki Cele ya ce kasar ta shaida mutuwar mutane 20,336 a bara, wanda kari ne idan aka kwatanta da irin lokacin a baya.
Cikin fushi ministan ya ce "hakan yana nufin ana kisan kai 57 a kowacce rana kamar ana yaki."
Bayanan 'yan sanda sun nuna cewa yawan kisan kai ya karu a cikin shekaru shida da suka gabata.
Francois Beukman, wanda ke jagorantar kwamiti na kula da 'yan sanda a majalisa dokokin kasar, ya bayyana yawan kisan a matsayin abin tsoro.
Ya yi kira ga 'yan kasar Afrika ta Kudu da kada su dauki hakan a matsayin al'ada mai kyau. "Dole ku gyara kasarku," in ji shi.
Ya yi alkawarin yin aiki tukuru don canja yanayin. Ya ce dole a warware wannan lamarin.
Ana alakanta yawan aikata kashe-kashen da ayyukan 'yan daba.